Ana zargin lalata a coci, IGP ya umarci ‘Yan Sanda su binciki Fasto Suleiman
- Ana zargin shugaban cocin Omega Fire Ministries International da aikata lalata
- Shugaban ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya bukaci a binciki Johnson Suleman
- Fasto Mike Davids ya na zargin tsohon Mai gidansa da kwanciya da Maidakinsa
Punch ta ce sufetan ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bada umarni a binciki shugaban cocin Omega Fire Ministries International, Apostle Johnson Suleman.
Ana zargin Apostle Johnson Suleman da laifin kwanciya da mai dakin Fasto Mike Davids, sannan ya ke yi wa ransa barazana, kuma ya hana shi ganin ‘ya ‘yansa.
Matar da ake zargin wannan babban Fasto da yin lalata da ita, ita ce Fasto Faith Edeko, wanda ita ma ta ke aiki a cocinsa na Omega Fire Ministries na reshen Utoka.
Shi kuma mai gidan wannan mata, Fasto Davids ya bar aiki a cocin da Suleman yake jagoranta.
KU KARANTA: Mai Garin da aka sace a Jihar Katsina ya na tsare a dajin Zamfara
Sufeta-Janar na ‘yan sanda ya aika wasika ta hannun Iliya Doma zuwa ga babban jami’in bincike a ranar 5 ga watan Junairu, 2021, ya na bada umarni a binciki faston.
Shugaban ‘yan sandan ya rubuta wannan takarda ne bayan wasu Lauyoyi; V.C Ezenagu & Associates sun kai karar Apostle Suleman a madadin Fasto Davids.
IGP ya bukaci jami’in ‘yan sanda dake kula da irin wadannan harkoki ya binciki zargin da ke kan malamin na lalata da mai aure da yi wa mai gidanta barazana.
A korafin da Davids ya rubuta, ya bayyana cewa ya hadu da Suleman tun ya na karatu a 2023, daga nan ya zama Fasto a cocinsa na tsawon shekaru 15 zuwa 2019.
KU KARANTA: Saraki ya fadi hanyoyin da za a bi a samu zaman lafiya da Makiyaya
Davids ya na kuka ya ce tun a sakandare ya hadu da maidakinsa, bayan shekaru 11 suna soyayya, sai suka yi aure, daga nan sai mai gidan na sa ya fara nemanta.
A karshen makon nan muka ji cewa 'yan bindiga sun harbe mai binciken kudin jihar Bauchi, Alhaji Abdu Aliyu bayan sunyi yunkurin sace shi a ranar Asabar.
Bayan haka sun sace wani matashin 'dansa mai shekaru 25 da wani mutum mai shekaru 51 da suke tafiya tare a lokacin da aka kai musu wannan harin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng