Yadda Minista Ya Yi Murabus duk da Tinubu Bai So Hakan ba
- Adebayo Adelayu wanda yake jagorantar ma'aikatar lantarki a Najeriya, ya yi murabus daga mukaminsa na Minista
- Ministan na lantarki ya yi murabus ne domin cika dadadden burin da yake da shi na zama gwamnan jihar Oyo a badi
- Majiyoyi sun bayyana cewa Adelabu ya yi murabus daga mukaminsa ne duk da cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bai so hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi murabus daga majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu.
Bayo Adelabu ya yi murabus ne duk da Shugaba Tinubu bai so hakan, inda ya yi ƙoƙarin lallaba shi kada ya bar aikin.

Source: Facebook
Wasu majiyoyi na kusa da suka san yadda dambarwar ta gudana kafin murabus ɗin, suka bayyana hakan ga jaridar The Punch a ranar Juma’a, 24 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Ganduje ya yi karatun ta natsu, ya gano dalilin da ya sa ake yawan samun mabarata a Arewa
Ministan wutar lantarki ya yi murabus
Majiyoyin sun bayyana cewa Adelabu ya dage kan barin majalisar ministocin ne domin ya biya buƙatarsa ta tsayawa takarar gwamna a jihar Oyo.
Jaridar Vanguard ta ce Adelabu ya sanar da murabus ɗinsa ne a ranar Laraba cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 22 ga Afrilu, 2026, wadda aka aika wa shugaban kasa ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).
Adelabu wanda ya tsaya takarar gwamna a jihar Oyo a ƙarƙashin jam’iyyar Accord a shekarar 2023 ya ce ya yi murabus ne domin ya ci gaba da fafutukar burinsa na zama gwamna.
Tinubu bai so murabus din Adelabu ba
Yayin da wani ɓangare na jama’a ke ganin cewa kila shugaban kasa ne ya buƙaci ministan ya yi murabus, majiyoyi na kusa sun dage cewa da kansa ya sauka domin ya nemi takarar gwamna.
Majiyoyi masu tushe a fadar shugaban kasa da kuma cikin hadiman Adelabu sun bayyana cewa Tinubu ya so ya naɗa shi a matsayin sabon Ministan kuɗi, biyo bayan murabus ɗin Wale Edun.
Wani babban jami'in gwamnati a fadar shugaban kasa ya bayyana cewa:
“Gaskiyar magana ita ce shi (Adelabu) ya yi murabus. Ba korarsa aka yi ba. Zan iya tabbatar muku da hakan. Hasali ma, shugaban kasa bai so ya tafi ba."
"Ya zo fadar shugaban kasa a ranar Talata, inda ya gana da Shugaban. Shugaban ya kwashe watanni biyu yana kauce masa don kada ya sami damar magana kan murabus. Shi ya sa ya jinkirta."

Source: Facebook
Tinubu ya yi wa Adelabu fatan alheri
A cewar majiyar, shugaban kasa ya tura wakilai don su gargaɗi Adelabu kan yin murabus.
“Shugaban kasa ya tura mutane su gaya masa kada ya yi murabus. Lokacin da mutanen biyu suka gana a fadar ranar Talata, Tinubu ya yi wa Adelabu tambaya kai tsaye game da damarsa ta cin zaɓen fitar da gwani da kuma na gwamna."
“Shugaban ya yi masa tambaya ta gaskiya: ‘Kana da tabbacin za ka samu tikitin?’ Shi kuma ya amsa nan take, ‘E, yallaɓai, zan iya ci. Zan yi nasara.’ Sai shugaban kasa ya ce masa, ‘Ina maka fatan alheri.’ Shi mutum ne mai fata na gari. Da kansa ya yi murabus."
- Wata majiya
Shugaban kasa ya rantsar da sabon Minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon Minista wanda zai yi aiki a gwamnatinsa.
Shugaba Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqa Rabe Darma, a matsayin sabon Ministan gidaje da raya birane bayan majalisar dattawa ta tabbatar da nadin da aka yi masa.
Mai girma Bola Tinubu, a cikin takaitaccen bayanin da ya yi yayin taron rantsuwar, ya taya Dr. Darma murna tare da bayyana shi a matsayin gwani a harkar gidaje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

