Akwai Kura: Faransa Ta Ja Kunnen 'Yan Kasarta kan Zuwa Yankuna 2 a Najeriya

Akwai Kura: Faransa Ta Ja Kunnen 'Yan Kasarta kan Zuwa Yankuna 2 a Najeriya

  • Faransa ta gargadi ‘yan kasarta kan zuwa wasu yankuna biyu na Najeriya saboda tsananin barazanar tsaro
  • Gwamnatin Faransa ta ce hare-haren kungiyoyin jihadi sun kara yaduwa zuwa wasu sassan Najeriya
  • Sace dalibai 39 a a jihar Oyo da 'yan ta'adda suka yi, ya nuna barazanar tsaro na kara matsawa zuwa Kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Paris - Faransa ta gargadi ‘yan kasarta cewa yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na Najeriya na fuskantar matsananciyar barazanar tsaro.

Faransa ta bukace su da su guji zuwa yankunan baki daya saboda hare-haren kungiyoyin jihadi masu haddasa asarar rayuka.

Faransa ta ja kunnen 'yan kasarta
Shugaban kasat Faransa, Emmanuel Macron Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Gwamnatin Faransa ta bayyana yankunan biyu a matsayin wuraren da ‘yan kasarta da masu ziyara daga Faransa bai kamata su je ba, kamar yadda aka sanya a shafin diplomartie.gouv.fr.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya koma kan matatun mai bayan karɓar tawagar NUPENG

A cikin shawarwarin tsaron, Faransa ta ce kungiyoyin jihadi sun sha kai munanan hare-hare a yankunan biyu, lamarin da ya sanya yin balaguro zuwa wuraren ke da matukar hadari.

Hare-haren da suka jawo gargadin

Hukumomin Faransa sun sake jaddada gargadin ne bayan wasu hare-hare da suka faru cikin watannin baya kuma suka kara tayar da hankula.

A ranar 3 ga Fabrairu, 2026, an kashe mutane da dama a kauyukan Woro da Nuku da ke jihar Kwara.

Fiye da makonni shida bayan haka, a ranar 16 ga Maris, 2026, an kai hari a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Faransa ta ambaci wadannan hare-hare a matsayin misalan da ke nuna cewa barazanar ta’addanci a Najeriya har yanzu tana da matukar tsanani.

Gwamnatin ta ce ‘yan kasarta su fahimci cewa akwai babban hadarin ayyukan ta’addanci a fadin Najeriya, yayin da yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ke cikin wuraren da ke da mafi girman hadarin.

Kara karanta wannan

Sojoji da jiragen yaƙi sun zafafa hare hare, sun rutsa yan bindiga ta sama da ƙasa a jihohi 2

Barazanar ta matsa Kudu

Baya ga yankunan Arewa, Faransa ta kuma nuna damuwa kan wani lamari da ya faru a watan Mayun 2026, lokacin da aka yi awon gaba da dalibai 39 da malamansu a jihar Oyo. Hukumomi sun danganta sace mutanen da kungiyoyin ta’addanci.

A cewar Faransa, lamarin ya nuna cewa barazanar tsaro ba ta takaita ga yankunan arewacin Najeriya kadai ba, domin yanzu tana kara matsawa zuwa wasu sassan kudancin kasar da a baya ake kallonsu a matsayin wuraren da suka fi samun kwanciyar hankali.

Gargadin Faransa bai bayyana tsawon lokacin da zai dauka ba, kuma bai fayyace irin sharuddan da za su sa a janye shi ba.

Faransa ta gargadi ‘yan kasarta da su guji Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na Najeriya saboda barazanar hare-haren kungiyoyin jihadi

Faransa ta gargadi 'yan kasarta kan Najeriya
Emmanuel Macron na jawabi a wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Faransa ta ja kunnen Israila

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya ce kasarsa ba za ta lamunci karuwar hare-haren da ake yi wa Kiristoci a Jerussalam ba.

Jean Noel-Barrot ya yi nuni da wani mummunan hari da aka kai wa wata malamar cocin Katolika ‘yar Faransa a Yammacin Kudus, wanda ya jawo bacin rai sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng