2027: An Fara Tsoron Sanatan APC zai Raunana Aikin Tinubu bayan Gana wa da Atiku Abubakar

2027: An Fara Tsoron Sanatan APC zai Raunana Aikin Tinubu bayan Gana wa da Atiku Abubakar

  • Ƙungiyar APC ta nuna damuwa kan rahoton ganawar sirri tsakanin Sanata Abdul’aziz Yari da jagororin adawa
  • An ce ganawar da ake zargi na iya aika saƙo mara kyau ga haɗin kan jam’iyya kafin babban zaɓen 2027 mai zuwa
  • Wannan damuwa na zuwa ne a lokacin da jam'iyyar APC ta fara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓe da ake shirin fafatawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Wata ƙungiya mai goyon bayan jam’iyyar APC, mai suna APC National Unity Support Group, ta bayyana damuwa kan rahotannin da ke cewa Sanata Abdul’aziz Yari ya yi wata ganawar sirri da manyan ‘yan adawa.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin waɗanda aka zauna da su har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda jigo ne a APC.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

An fara tsoron sakamakon ganawar Yari da Atiku
Sanatan Zamfara ta yamma, AbdulAziz Yari Hoto: AbdulAziz Yari
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da mai tsara ayyukan yankin ƙungiyar, Dakta Haruna Sadauki, ya fitar a ranar Laraba 22 Afrilu 2026 a Abuja, an ce akwai damuwa.

Ƙungiyar APC ta damu kan Abdulaziz yari

Jaridar Thisday ta wallafa cewa Dakta Haruna Sadauki ya bayyana wannan batu a matsayin abin da ke tayar da hankali.

Ya yi gargadin cewa hakan na iya aika saƙo mara kyau game da haɗin kan jam’iyyar yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Ya ce:

“Mun damu ƙwarai da waɗannan rahotanni. A daidai lokacin da jam’iyya ke ƙoƙarin ƙarfafa kanta da haɗin kai a ciki, irin waɗannan zarge-zargen ganawa da ‘yan adawa na haifar da tambayoyi masu yawa.”

Kiran ƙungiyar APC ga Sanata Yari

Ƙungiyar ta kuma yi kira ga Sanata Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, da sauran ‘yan jam’iyya da su guji abin da ta kira hulɗar sirri da ka iya raunana zaman lafiyar jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji da tsohon minista suka raba miliyoyin Naira don kifar da gwamnatin Tinubu

A cewar sanarwar, irin wannan mu’amala—idan aka tabbatar—na iya karkatar da hankali daga manufofi da sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ƙoƙarin aiwatarwa.

Ana tsoron Yaro zai kawo cikas ga kokarin Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata AbdulAziz Yari Hoto: @officialABAT/@IU_Wakilii
Source: Twitter

Ƙungiyar ta jaddada cewa gwamnatin Tinubu na mai da hankali wajen bunƙasa ci gaba mai ɗorewa da haɗin kan ƙasa, tana mai cewa duk wani mataki da zai nuna sabani na iya rage amincewar jama’a da haɗin kan jam’iyya.

Duk da amincewa da irin tasirin da Yari ke da shi a APC a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar, ƙungiyar ta ce wannan rahoto ya haifar da muhawara kan biyayyarsa da kuma alkiblar siyasarsa a gaba.

Tinubu ya sa labule da gwamnonin APC

A baya, mun wallafa cewa bayan ganawa da sanatoci, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ganawar sirri da gwamnonin APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Taron ya samu halartar gwamnoni da dama daga ciki har da Hope Uzodimma, Inuwa Yahaya da Babagana Zulum yayin da ake sa ran tunkarar zaɓe mai zuwa.

Daga cikin abubuwan da aka tattauna a kan batun bayar da tikitin takara kai tsaye, lamarin da aka cimma matsaya kan hanyoyi biyu na fitar da masu neman takara a APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng