Ministan Buhari da EFCC Ke Tuhuma kan Zambar N2.8bn Zai Fito Takara a Katsina

Ministan Buhari da EFCC Ke Tuhuma kan Zambar N2.8bn Zai Fito Takara a Katsina

  • Tsohon minista, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar sanatan Katsina ta Arewa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC
  • Hadi Sirika ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne sakamakon matsin lamba da kiraye-kiraye da yake samu daga al’ummar shiyyar Daura
  • Wannan na zuwa ne yayin da Sirika ke ci gaba da fuskantar shari’a a gaban kotu bayan EFCC ta gurfanar da shi kan zargin almundahanar N2.8bn

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana aniyarsa a hukumance ta neman kujerar sanata mai wakiltar shiyyar Katsina ta Arewa a zaɓen 2027.

Sirika ya zaɓi tsayawa takarar ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC, inda yake fatan komawa majalisar da ya taɓa zama a cikinta.

Kara karanta wannan

2027: An fara zargin Obi zai yaudari 'yan Arewa saboda ya muzguna masu a baya

Hadi Sirika ya sanar da kudurinsa na fitowa takarar sanata a shiyyar Daura, jihar Katsina
Sanata Hadi Sirika (tsakiya) ya na gaisawa da magoya bayansa a yayin kaddamar da aniyarsa ta yin takarar sanata a shiyyar Daura. Hoto: Katsina Post
Source: Facebook

Hadi Sirika zai tsaya takarar sanata

Sanarwar ta fito ne a ranar Juma'a, 24 ga watan Afrilu, 2026, daga mai tallafa wa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Imran Muhammad, a shafinsa na X.

Majiyoyi na kusa da tsohon ministan sun tabbatar da cewa Sirika ya riga ya fara tuntubar shugabannin jam'iyya na matakin gundumomi da ƙananan hukumomi da ke shiyyar ta Daura.

Sirika ya bayyana aniyarsa ne a hukumance yayin wata ziyara da ya kai sakatariyar jam’iyyar APC ta jihar Katsina a yau Juma’a, 24 ga watan Afrilu, 2026.

Ziyarar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ta kammala shirye-shiryen fara sayar da fom ɗin takara ga masu sha’awa tun daga ranar Asabar, 25 ga Afrilu.

Sanata Sirika ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin yin takara a ƙarƙashin jam’iyya mai mulki domin wakiltar mutanen shiyyar Daura.

Hadi Sirika ya fadi dalilin son yin takara

Kara karanta wannan

2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar

A wani rahoto da Katsina Post ta wallafa a shafinta na Facebook, an ji Hadi Sirika yana cewa ya dauki wannan mataki ne sakamakon kiraye-kirayen da yake samu daga al’ummar yankin, wanda hakan ya sa ya ga dacewar fitowa fili domin neman amincewar jama’a.

Ya bayyana APC a matsayin jam’iyya mai hadin kai da tsari, tare da yabawa shugabanninta bisa yadda suke tafiyar da al’amura cikin inganci da kwarewa.

Sirika ya jaddada cewa, ko kafin ya rike mukamin sanata, ya taba aiwatar da ayyukan ci gaba a yankin Daura da kewaye, yana mai cewa al’umma su ne shaida kan irin wadannan ayyuka.

A cewarsa, wannan ne ya kara masa kwarin gwiwa wajen sake neman wannan dama, ya kuma yi alkawarin cewa idan aka zabe shi a matsayin sanata, zai kara bunkasa ayyukan raya kasa tare da fadada su fiye da yadda aka gani a baya.

Hadi Sirika ya ayyana tsaya wa takarar sanata yayin da yake tsakiyar shari'a da EFCC kan zargin almundahana
Sanata Hadi Sirika, tsohon minista da ke shari'a da EFCC kan badakalar N2.8bn. Hoto: Hadi Sirika, Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Shari'ar EFCC da Hadi Sirika

Duk da wannan yunkuri na siyasa, takarar Sirika tana fuskantar wani babban ƙalubale na shari'a. Hukumar EFCC tana tuhumar sa tare da wasu iyalansa da kamfanin Al Buraq Global Investment Limited kan zargin karkatar da kuɗaɗe kusan naira biliyan 2.8.

Kara karanta wannan

Sabon salo: APC ta faɗi tsari 2 da za ta yi amfani da su wajen zaɓen ƴan takara

Ana zargin an tafka maguɗin ne wajen kwangilar faɗaɗa filin jirgin saman Katsina, kamar yadda rahoton jaridar The Premium Times ya nuna.

Sirika: Kotu ta ki karbar shaidar EFCC

A wani labari, mun ruwaito cewa, babbar kotun Abuja ta yi watsi da wasu muhimman hujjoji da hukumar EFCC ta gabatar mata kan tuhumar Sanata Hadi Sirika.

Hukumar ta yi watsi da hujjojin ne a shari’ar zargin damfarar kwangilar N2.8bn da ake yi wa tsohon ministan sufurin jiragen sama,huk Hadi Sirika.

Mai shari’a Sylvanus Oriji ya ce ba a bi tanadin sashe na 15(4) na dokar ACJA 2015 ba wajen karɓar waɗannan bayanai wanda hakan ya saba doka matuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com