Dan takarar shugaban kasa ya ba PDP sa’o’i 48 don ta ajiye Atiku sannan ta sake zaben fidda gwani

Dan takarar shugaban kasa ya ba PDP sa’o’i 48 don ta ajiye Atiku sannan ta sake zaben fidda gwani

Mista Stanley Osifo, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya ba jam’iyyar wa’adin sa’o’i 48 don ta soke zaben fidda gwaninta, inda ya nemi aui sabon zaben fidda dan takara.

Osifo ya kumayi barazanar zuwa kotu idan jam’iyyar ta ki soke zaben fidda gwaninta wanda ya kai ga har ta tsayar da Atiku a matsayin dan takararta.

Da yake jawabi ga manema labarai a Lagas, Osifo ya bayyana cewa ya cancanci a bashi dama kamar yadda aka baiwa sauran yan takara a jam’iyyar, tunda har ya siya fam din nuna ra’ayin takara akan naira miliyan 12.

Dan takarar shugaban kasa ya ba PDP sa’o’i 48 don ta ajiye Atiku sannan a sake zaben fidda gwani

Dan takarar shugaban kasa ya ba PDP sa’o’i 48 don ta ajiye Atiku sannan a sake zaben fidda gwani
Source: Facebook

Dan takarar wanda ya fito daga Edo yace babbar matsalar shi shine cewar ba’a bari an tantance shi ba sannan kuma aka hana mashi yin zaben fidda gwani ba tare da wani hujja ba.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019 tsakanin barayi da masu gaskiya ne – El-Rufai

Ya bayyana cewa ba’a yi masa adalci ba.

Osifo yacce babu wanda ya sanya shi kawai so yake ya karbi hakkinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel