Zabe Ya Fara Zafi: Yan Daba Sun Watsa Jama’a a Mazabar Ministan Buhari

Zabe Ya Fara Zafi: Yan Daba Sun Watsa Jama’a a Mazabar Ministan Buhari

  • An samu rikici a kada kuri’a a rumfar tsohon gwamnan Osun kuma tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola
  • Rahotanni sun ce ‘yan daban sun kori masu kada kuri’a daga rumfar, lamarin da ya haifar da fargaba tare da dagula tsarin zaben gwamnan
  • Hukumar INEC da jami’an tsaro ba su bayyana cikakken bayani kan lamarin ba, yayin da ake ci gaba da jiran matakan da za a dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - An samu tangarda a kada kuri’a a rumfar tsohon gwamnan Osun kuma tsohon ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola.

Majiyoyi sun ce ana zargin ‘yan daba sun tarwatsa masu kada kuri’a tare da dagula tsarin zaben.

An tarwatsa masu zabe a Osun
Jami'an yan sanda a bakin aiki da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola. Hoto: Nigeria Police Force, Rauf Aregbesola.
Source: Twitter

Osun: An shiga fargaba bayan tarwatsa masu zabe

Lamarin ya haifar da tashin hankali a rumfar kada kuri’ar, inda rahotanni suka ce an tilasta wa masu kada kuri’a barin wurin yayin da yanayin wurin ya fara tabarbarewa, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Manyan laifuffukan zabe a Najeriya da hukuncin da doka ta tanada

Wannan lamari ya kawo cikas ga tsarin kada kuri’a tare da haifar da damuwa kan yadda zaben gwamnan ke gudana a yankin.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a rumfar da ke da alaka da tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, wanda ya taba rike mukamin ministan cikin gida.

An ce wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun shiga wurin kada kuri’ar, inda suka tarwatsa masu kada kuri’a tare da hana gudanar da aikin zabe cikin kwanciyar hankali.

Saboda lamarin, yanayin wurin ya sauya, yayin da masu kada kuri’a suka bar rumfar domin tsira daga duk wani abin da zai iya jefa rayukansu cikin hadari.

An fara kai ruwa rana a zaben gwamnan Osun
Taswirar jihar Osun da ake gudanar da zabe a yau Asabar. Hoto: Legit.
Source: Original

Ana ci gaba binciken gano masu laifi a lamarin

Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan musabbabin lamarin ko wadanda ake zargin sun shirya shi ba.

Haka kuma, ba a samu cikakken bayani kan martanin jami’an tsaro ko matakan da hukumomin zabe suka dauka domin dawo da zaman lafiya a wurin ba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza da Lakurawa 300, an rasa rayuka bayan yin jina jina

Lamarin ya janyo damuwa game da yadda zaben gwamnan Osun ke gudana, musamman kan batun tsaro da damar masu kada kuri’a na gudanar da hakkinsu cikin 'yanci.

Ana ci gaba da jiran karin bayani daga hukumomin tsaro da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, kan abin da ya faru da matakan da za a dauka.

Hakan ya jefa fargaba a zukatan masu zabe yayin da wasu suke ganin ya kamata su koma saboda tsira da rayukansu.

Osun: Kananan hukumomi da ka iya yin tasiri

An ji cewa zaben gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta ya fi karkata kan Ademola Adeleke, Bola Oyebamiji da Najeem Salaam, wadanda duk suka fito daga Osun ta Yamma.

Osogbo, Olorunda, Ife Central, Ife ta Gabas, Ife ta Kudu, Odo Otin, Iwo da Ilesa ta Gabas na cikin manyan kananan hukumomin jihar.

Adeleke na dogaro da ayyukan raya kasa da karfin Ede, yayin da Oyebamiji da Salaam ke neman samun gagarumar nasara a wasu muhimman kananan hukumomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.