Turkiyya Ta Yi wa Ƙasashen Turai Mummunan Albishir kan Yaƙin Rasha

Turkiyya Ta Yi wa Ƙasashen Turai Mummunan Albishir kan Yaƙin Rasha

  • Shugaban kasar Turkiyya, Raccep Tayyib Erdogan ya gargadin cewa yaƙin Rasha da Ukraine na raunana nahiyar Turai
  • Erdogan ya ce rashin mayar da hankali kan zaman lafiya zai ƙara jawo wasu matsaloli da zai taba dukkanin kasashen yankin
  • Ya jaddada ƙoƙarin Turkiyya na kawo ƙarshen rikicin da ya shafe tsawon lokaci tsakanin https://admin.legit.ng/posts/1706768asashen biyu ta hanyar tattaunawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Turkey – Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa yaƙin da ke tsakanin Rasha da Ukraine ya fara raunana ƙasashen Turai.

Shugaban ya yi gargadin cewa za a fuskanci gagarumar matsala nan gaba kaɗan matukar ba a rungumi hanyar zaman lafiya ba.

Erdogan ya gargadi Turai kan yakin Rasha da Ukraine
Shugaban kasar Turkiyya, Raccep Tayyib Erdogan Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta wallafa cewa Erdogan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawar waya da shugaban ƙasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan

"Kada ku bar Turawa su yaudare ku": Gumi ya shawarci gwamnati kan sulhu da ƴan ta'adda

Turkiyya ta magantu kan yakin Rasha da Ukraine

Anadolu Ajansi ta wallafa cewa Raccep Tayyib Erdogan ya ce, idan aka ci gaba da tafiya ba tare da an mayar da hankali kan sulhu da tattaunawa ba, rikicin zai ƙara tsananta tare da janyo illa mai yawa ga yankin Turai baki ɗaya.

A cewarsa, yaƙin ya riga ya fara nuna tasiri a fannonin tattalin arziƙi da tsaro a Turai, lamarin da ke buƙatar gaggawar dauƙar matakai na diflomasiyya domin dakatar da rikicin.

Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsaloli da dama a yankin sakamakon dogon rikicin ƙasashen biyu.

Kasar Turkiyya na ƙoƙarin a yi sulhu

A yayin tattaunawar, shugaban ya kuma bayyana cewa dangantaka tsakanin Turkiyya da Jamus ta samu inganta kuma an samu ci gaba a ‘yan kwanakin nan, musamman ta hanyar mu’amala tsakanin manyan jami’an gwamnatoci biyu.

Ya ƙara da cewa, Turkiyya na ci gaba da taka rawar gani wajen neman kawo karshen yaƙin tsakanin Rasha da Ukraine ta hanyar tattaunawa, domin cimma zaman lafiya mai dorewa.

Kara karanta wannan

Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

A cewarsa, wannan mataki ya yi kama da irin ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen warware rikicin da ya shafi Iran da Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Erdogan ya jaddada cewa hanya mafi dacewa ita ce ta sulhu da tattaunawa, yana mai cewa amfani da karfi kadai ba zai kawo karshen rikicin ba.

Turkiyya ta ce yana kokarin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine
Shugaban Rasha Vladimir Putin, da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky Hoto: MIKHAIL METZEL/POOL/AFP, Antonio Masiello/Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce burin Turkiyya shi ne ganin an samu mafita mai dorewa da za ta kawo zaman lafiya ga yankin da ma duniya baki ɗaya.

Haka kuma, ya nuna cewa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasiri kamar Turkiyya da Jamus na da muhimmanci wajen samar da mafita ga rikice-rikicen duniya

Ministan Turkiyya ya gano shirin Isra'ila

A baya, kun ji cewa ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya yi gargadin cewa Isra’ila na iya mayar da hankali kan wata kasar a Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila ta sako Iran a gaba har ta kai ta hada kai da Amurka wajen kai harin da ya kashe jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamnei a farkon shekarar 2026.

Hakan Fidan ya bayyana damuwa kan hare-haren Isra’ila a Lebanon da Syria, tare da yiwuwar barazana ga yankin Gabas ta Tsakiya baki daya idan ba a tashi tsaye ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng