ADC Ta Zargi APC da Shirin Hana Taron Tsara Kawar da Tinubu a 2027
- Babbar jam'iyyar adawa ta ADC ta yi zargin cewa APC na shirin hana taron ‘yan adawa da aka tsara za a yi a birnin Ibadan na jihar Oyo
- Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya sanar da cewa a yau Asabar, 25 ga watan Afrilun 2026 aka tsara za a gudanar da taron
- Tun a lokacin babban taron ADC na kasa a Abuja sakataren jam'iyyar ya sanar da cewa 'yan adawa za su yi wani muhimmin taro a Oyo
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Jam’iyyar ADC ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da kokarin kawo cikas ga taron ‘yan adawa da ake shirin gudanarwa a Ibadan, Jihar Oyo.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan adawa ke cigaba da korafi kan cewa gwamnatin APC na da niyyar hana jam'iyyun hamayya tasiri a zaben 2027.

Source: Facebook
Zargin da ADC ta yi wa jam'iyyar APC
Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ne ya yi korafi a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce sun gano wani shiri na kawo cikas ga taron da aka tsara gudanarwa a ranar 25 ga Afrilun 2026.
Ya ce:
“Mun gano shirye-shiryen da jam’iyyar APC ke yi na kawo cikas ga taron ‘yan adawa da za a yi a Ibadan.”
Sai dai Malam Bolaji Abdullahi ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta ja da baya ba duk daa bin da ta gano APC na shirin kulla mata.
Zargin hana jam'iyyar ADC wajen taro
Ya kara da cewa jam’iyya mai mulki na yawan kawo cikas ga ayyukan ‘yan adawa, yana mai cewa a baya ma an hana su amfani da wuraren taro a Abuja.
“Bayan sun hana mu amfani da wurare a Abuja, yanzu ma ba sa son mu gudanar da taronmu cikin kwanciyar hankali,”
In ji shi.
Bolaji Abdullahi ya ce duk da cewa APC na ikirarin ba ta jin tsoron ‘yan adawa, amma halayenta na nuna akasin haka:
“Sun ce ba su jin tsoro, amma ayyukansu na nuna kamar suna cikin firgici,”
Duk da haka, ya tabbatar da cewa jam’iyyun adawa za su ci gaba da shirinsu na gudanar da taron kamar yadda suka tsara a Ibadan
“Ba za mu fasa ba, domin muna tare da al’ummar Najeriya,”
In ji Bolaji Abdullahi
Bayani kan taron 'yan adawa
A makon da ya wuce, sakataren jam’iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa jam’iyyun adawa na shirin gudanar da babban taro na hadin gwiwa domin tsara yadda za su tunkari zaben 2027.

Source: Facebook
Premium Times ta wallafa cewa Aregbesola, wanda tsohon gwamnan Jihar Osun ne, ya ce manufar taron ita ce karfafa hadin kai tsakanin jam’iyyun adawa da kuma samar da tsari guda domin kalubalantar Bola Tinubu da APC.

Kara karanta wannan
2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar
Maganar neman rusa tafiyar ADC
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bukaci a tarwatsa jam'iyyar ADC.
Gbajabiamila ya yi magana ne yayin bikin murnar ranar haihuwa a gidan wani dan majalisar wakilai da ya ke jam'iyyar adawa ta ADC a Abuja.
Ya bukaci dan majalisar da Nafiu Bala da kar su sauya sheka, su tsaya su kawo rikicin da za su hana jam'iyyar ADC sakat a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

