Jam'iyyar ADC Ta Kara Girma, Ta Karbi Kujera Mai Gwabi a Majalisar Dattawan Najeriya
- Jam'iyyar hadaka ta ADC ta karbi kujerar mai tsawatarwa na bangaren 'yan adawa a Majalisar dattawa yayin da take kara karfi
- Shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya sanar da nadin Sanata Tony Nwoye na ADC a matsayin mai tsawatarwa na marasa rinjaye
- Rahotanni sun nuna cewa ADC ta zama babbar jam’iyyar adawa a majalisar dattawa, inda take da sanatoci tara, yayin da PDP ke da guda biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam'iyyar hadaka, ADC ta fara samun kujerun shugabanci a Majalisar dattawa ta 10 bayn sauya shekar wasu sanatoci a Najeriya.
Majalisar dattawan Najeriya ta nada Sanata Tony Nwoye na jam’iyyar ADC a matsayin sabon mai tsawatarwa na marasa rinjaye.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa nadin ya biyo bayan murabus din tsohon mai rike da wannan mukami, Sanata Osita Ngwu, wanda ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Yadda 'dan ADC ya samu mukami
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ya sanar da nadin, inda ya ce takardar nadin Sanata Nwoye ta fito ne daga bangaren ‘yan adawa na majalisar.
Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ADC ta zama babbar jam’iyyar adawa a majalisar dattawa, inda take da sanatoci tara, yayin da PDP ke da guda biyar.
Duk da wannan sauyi, majalisar ba ta yi bayani ba kan matsayin Sanata Abba Moro na PDP ba, wanda har yanzu ke ci gaba da zama shugaban marasa rinjaye.
ADC ta zama babbar jam'iyyar adawa
Wani masani kan harkokin siyasa, John Oloriegbe, ya bayyana cewa ya dace ADC ta gabatar da sabon shugaban marasa rinjaye, kasancewar ita ce babbar jam’iyyar adawa a yanzu.
“Ban fahimci dalilin da ya sa Abba Moro ke ci gaba da zama a kujerar shugaban marasa rinjaye ba, alhali jam’iyyarsa ba ita ce mafi rinjaye a bangaren ‘yan adawa ba,” in ji shi

Kara karanta wannan
Bayan sauya shekar Kwankwaso, wasu manyan jiga jigan siyasar Najeriya za su koma ADC
Sai dai ya kara da cewa wannan sauyi zai dogara ne kan ko sanatocin ADC sun mika bukata a hukumance ga shugabancin majalisa ko a'a, cewar Channels tv.

Source: Facebook
Sauye-sauyen jam’iyyu
A zaman majalisar, an samu karin sauye-sauyen siyasa, inda Sanata Anthony Siyako Yaro (Gombe ta Kudu) ya fice daga PDP zuwa APC, yana mai danganta hakan da rikicin shugabanci a jam’iyyarsa ta baya.
Haka kuma, Sanata Ahmed Aliyu Wadada (SDP, Nasarawa ta Yamma) ya sanar da majalisar cewa ya koma APC, yana mai cewa ya dauki wannan mataki tun a watan Agustan 2025 sakamakon rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar SDP.
Sanatan ADC ya roki Atiku ua janye
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Victor Umeh ya ce ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya hakura da neman takara a babban zaben 2027.
Sanata Umeh, xaya daga cikin sanatocin da suka rungumi ADC, ya ce ya kamata Atiku Abubakar ya yi la’akari da shekarunsa, ya janyewa matasa ‘yan siyasa.
Ya ƙara da cewa matasan Najeriya na bukatar su koyi dabarun jagoranci daga hannun tsofaffin shugabanni kuma su fara samun ƙwarewa.
Asali: Legit.ng
