Cin Bashi: Fadar Shugaban Kasa Ta Yi wa Sanusi II Martani kan Sukar Tinubu
- Fadar shugaban kasa ta yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II martani kan caccakar gwamnatin Bola Tinubu da ya yi game da ciwo bashi
- Sarkin ya yi magana ne bayan shugaba Bola Tinubu ya tura wasikar neman a sahale masa ya ciwo bashin $516.3m a majalisar dattawa
- Tun bayan bullar labarin wasikar shugaban kasar, 'yan Najeriya da dama sun yi korai game da ciwo bashin duk da cewa an cire tallafin mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Muhammadu Sanusi II da Fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan yadda bashin Najeriya ke karuwa, bayan sabon gargadin da Sarkin ya yi game da ci gaba da karbar bashi a gwamnatin Bola Tinubu.
Sanusi II, wanda tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ne, ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke yawan dogaro da rance duk da cire tallafin mai.

Kara karanta wannan
Sanusi II ya magantu kan yawan cin bashin Gwamnatin Tinubu duk da cire tallafin fetur

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa bayanin Sanusi II ya zo ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan sabon bukatar bashin da shugaban kasa ya mikawa majalisar dattawa, inda ya nemi amincewa da neman rancen dala miliyan 516.3
Rahotanni sun nuna cewa zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025, jimillar bashin gwamnati ya kai Naira tiriliyan 159.28, bisa bayanan da Hukumar Kula da Bashin Kasa ta fitar.
Martanin fadar shugaban kasa
Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani ta bakin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, inda ya kare matakin karbar bashin, yana cewa za a aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa ne.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Bwala ya ce bangaren abubuwan more rayuwa a Najeriya yana bukatar ware masa kudi mai yawa a kowace shekara.
Ya ce:
“Muna karbar bashi ne domin saka hannun jari a muhimman bangarorin tattalin arziki, musamman bangaren gine-gine. Najeriya na bukatar tsakanin dala biliyan 30 zuwa 100 a duk shekara, kuma abin da ake da shi a kasa bai isa ba.”

Source: Twitter
Bayani masana kan bashin gwamnati
A gefe guda kuma, masana tattalin arziki sun rabu gida biyu kan wannan muhawara, inda wasu suka goyi bayan korafin da sarkin ya yi.
Wani masani fannin tattalin arziki a Jami’ar Uyo, Paul Orebiyi, ya tambayi yadda aka yi amfani da kudin da aka samu bayan cire tallafin mai, yana gargadin cewa bai kamata a rika kashe su ba tare da gani a kasa ba.
Shi ma wani masani, Akin Akinleye, ya yi gargadi da cewa ci gaba da karbar bashi na iya kara jefa tattalin arzikin kasar cikin matsin lamba.
Raddin fadar shugaban kasa ga Atiku
A wani labarin, mun kawo muku cewa fadar shugaban kasa ta yi martani ga Atiku Abubakar da ya ce ba makawa zai yi takara a zaben 2027.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce idan Atiku ya yi haka ya rusa tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa.
Sai dai Atiku Abubakar ya sha bayyana cewa tsarin karba-karba ba shi da alaka da kundin mulkin Najeriya, ra'ayi ne kawai na jam'iyyu.
Asali: Legit.ng
