Hadi Sirika: EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Ministan Buhari Kan Badakalar N19.4bn

Hadi Sirika: EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Ministan Buhari Kan Badakalar N19.4bn

  • Hukumar yaƙi da cin hamci ta EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu
  • Hukumar EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika ne tare da ɗan'uwansa, Ahmad Abubakar Sirika da wani kamfani kan badaƙalar N19.4bn
  • Waɗanda ake ƙarar dai sun musanta aikata tuhume-tuhumen da hukumar yaƙi da masu wawushe dukiyar al'umma ke yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama a gaban kotu.

Hukumar EFCC na zargin tsohon ministan da yin almundahanar kwangiloli lokacin da yake ofis.

EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika a kotu
EFCC na tuhumar Hadi Sirika kan badakalar N19.4bn Hoto: @TosinOlugbenga
Asali: Twitter

An gurfanar da Hadi Sirika ne tare da ɗan'uwansa Ahmad Abubakar Sirika, da kamfanin Enginos Nigeria Limited mallakin Ahmad Abubakar Sirika, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Ebrahim Raisi: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba kan shugaban ƙasar Iran da ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuhumar EFCC kan Hadi Sirika

An dai gurfanar da su ne kan tuhume-tuhume 10 da aka gyara a ranar 14 ga watan Mayu 13 kuma aka shigar gaban kotu a ranar 14 ga watan Mayu, 2024.

Ana zargin Hadi Sirika da amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba wajen bayar da kwangiloli na Naira biliyan 19.4 ga kamfanin Enginos Nigeria Limited.

Sirika sun ce ba su da laifi

Waɗanda ake tuhumar dai sun musanta aikata dukkanin laifukan da ake tuhumarsu da su, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

A ranar 14 ga watan Mayu, shari'ar da ake yi wa Hadi Sirika ta tsaya saboda waɗanda ake ƙarar ba su halarci zaman kotun ba.

Ana kuma tuhumar tsohon ministan bisa wasu zargi guda shida da ke da alaƙa da laifuffuka iri ɗaya.

Kara karanta wannan

Ana murnar Notcoin ya fashe, kotun tarayya ta yanke hukunci kan jami'in Binance a Najeriya

Hadi Sirika ya kasance ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Hukumar EFCC ta fara binciken badaƙalar kwangila a kan Hadi Sirika tun kafin ya bar ofis.

Hadi Sirika ya shirya zuwa kurkuku

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika wanda ke fuskantar shari'a kan zargin badaƙalar N2.8bn, ya nuna cewa a shirye yake ya je gidan kurkuku.

Tsohon ministan ya nuna alamun hakan ne lokacin da yake kwantar da hankalin ɗiyarsa a kotu inda ya ba da misali da cewa har Annabawa an taɓa kullewa a gidan kurkuku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel