Babban Labari: Shugaban Faransa zai Kawo Ziyara Najeriya
- Jakadan Faransa ya sanar da cewa Shugaba Emmanuel Macron zai kawo ziyarar aiki Najeriya a kwanaki masu zuwa
- Ziyarar za ta zo ne shekaru biyu bayan da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki Paris
- Jakadan ya ce zaman da Macron ya yi a Najeriya a matsayin ɗalibi ya taimaka masa wajen fahimtar nahiyar Afrika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jakadan Faransa a Najeriya da ƙungiyar ECOWAS, Marc Fonbaustier, ya sanar da cewa Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, zai kawo ziyarar aiki zuwa Najeriya.
Ya bayyana cewa ziyarar za ta bai wa ƙasashen biyu damar duba irin ci gaban haɗin gwiwarsu da kuma tsara sabbin hanyoyin ƙarfafa dangantaka a nan gaba.

Source: Twitter
Punch ta bayyana cewa Fonbaustier ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin Ranar Ƙasa ta Faransa da aka gudanar a daren Talata a Abuja.
Shugaban Faransa zai zo Najeriya
Da yake bayyana abin da ya kira labari na musamman, jakadan ya ce ziyarar Macron za ta gudana ne shekara biyu bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai irin wannan ziyarar aiki zuwa birnin Paris.
Ya ce:
“Shugabannin ƙasashenmu biyu za su tantance irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da taswirar haɗin gwiwarmu, sannan su tsara muhimman abubuwan da za su jagoranci dangantakarmu a shekaru masu zuwa. Babu shakka, wannan zai amfani al’ummomin ƙasashen biyu.”
Jakadan ya ce dangantakar Najeriya da Faransa ta ginu ne bisa daidaito, yana mai jaddada cewa ƙasashen biyu na kallon juna a matsayin abokan hulɗa masu martaba iri ɗaya.
Alakar Najeriya da Faransa
Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana cewa haɗin gwiwar Najeriya da Faransa ba a baki kawai take ba, haɗin gwiwa ce tsakanin ƙasashe masu martaba iri ɗaya.
Ta ce:
“A dangantakarmu ta ƙasashe biyu, wannan na nufin kauce wa son zuciya, rashin tilastawa juna wani abu, da kuma rashin tsoma baki cikin harkokin juna.
"Maimakon haka, yana nufin sauraron juna, tattaunawa da buɗaɗɗiyar zuciya, da yanke shawara tare.
Fonbaustier ya ce ƙasashen biyu suna da muradun bai ɗaya na bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa, samar da ayyukan yi, da kare muhalli.

Source: Facebook
Jaridar Blueprint ta wallafa cewa ya ce:
“Muna son ci gaban tattalin arziki da zamantakewar ƙasashenmu domin amfanin al’ummominmu, samar da ayyukan yi, inganta rayuwar jama’a tare da kiyaye muhalli, halittu, ruwa da iska.”
Macron ya zauna a Najeriya
Jakadan ya kuma bayyana cewa hangen nesa na Macron game da Afirka ya samo asali ne daga zaman da ya yi a Najeriya na tsawon watanni shida a matsayin ɗalibi shekaru 24 da suka gabata.
Ya ce:
“Sabuwar dangantakar Faransa da Afirka ta fara ne a Najeriya, ko kuma a ce an ƙirƙire ta ne a Najeriya. Domin Emmanuel Macron ya shafe watanni shida masu muhimmanci a wannan ƙasa lokacin yana ɗalibi shekaru 24 da suka wuce."
An doke Faransa a kofin duniya
A wani labarin, mun kawo muku cewa kasar Faransa ta sha kashi a hannun 'yan kwallon kasar Spain a wasan da suka buga.
Hakan na zuwa ne bayan an shafe mintuna sama da 90 ana fafatawa, inda aka tashi da ci 2-0 sakamakon kwallayen da Spain ta zura.
Wasan ya kawo karshen burin Faransa na lashe kofin duniya da ake yi a yanzu haka a kasar Amurka, inda jirginsu zai koma gida.
Asali: Legit.ng


