Ta Faru Ta Kare: Kotu Ta Kwace Kadarori 48 na Malami a Abuja, Kano da Wasu Jihohi
- Babbar Kotun Tarayya ta amince da bukatar EFCC, ta ba da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake alaƙanta wa tsohon minista, Abubakar Malami
- Alƙaliyar kotun ta ce Abubakar Malami da masu ikirarin mallakar kadarorin sun gaza tabbatar da cewa sun mallake su ta da kudin halal
- Hukuncin ƙwace kadarorin bai zama hukuncin aikata laifi ba, yayin da ake ci gaba da shari'ar zargin halasta kuɗaɗen haram kan Malami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin ƙwace kadarori 48 da ake alaƙanta wa tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami.
Rahotanni sun bayana cewa kadarorin suna jihohin Abuja, Kano, Kebbi da Kaduna.

Source: Twitter
EFCC ta kwace kadarorin Malami
Mai shari'a Joyce Abdulmalik ta amince da buƙatar EFCC bayan ta yanke hukuncin cewa Malami da sauran mutanen da suka yi ikirarin mallakar kadarorin sun kasa gabatar da hujjojin da ke nuna cewa sun mallake su ta hanyar da ta dace, in ji rahoton The Nation.
Kafin yanke hukuncin, kotun ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe da buƙatun da Malami da wasu 'yan uwansa da kuma kamfanoni masu alaƙa da kadarorin suka gabatar.
Kotun ta bayyana cewa abin da take dubawa ba wai wanene ya mallaki kadarorin ba ne, illa yadda aka samu kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen sayen su.
Ta ce masu ƙalubalantar buƙatar EFCC sun kasa kawar da zargin cewa an mallaki kadarorin ne ta hanyar ayyukan da ba su dace da doka ba.
Mai shari'a Abdulmalik ta jingina hukuncinta ne da Sashe na 17 na Dokar Advance Fee Fraud and Other Fraud Related Offences Act, wanda ya ba ta damar bayar da umarnin ƙwace kadarorin har abada.
Asalin shari'ar EFCC da Malami
EFCC ta shigar da ƙarar ne tun a watan Janairun 2026 tana neman a ƙwace kadarori 57 da darajarsu ta kai Naira biliyan 212.8, tana zargin cewa kuɗaɗen da aka saye su da su sun samo asali ne daga haramtattun ayyuka.
Bayan kotu ta bayar da umarnin ƙwace na wucin gadi, Malami da matarsa Nana Hadiza Malami da ɗansa Abdulaziz Abubakar Malami tare da wasu kamfanoni suka ƙalubalanci matakin, suna mai cewa an mallaki kadarorin ne bisa doka kuma EFCC ba ta tabbatar da alaƙarsu da wata haramtacciyar hanya ba.

Source: Getty Images
Ana ci gaba da wata shari'a
Punch ta ruwaito cewa ko da yake kotun ta ba da umarnin ƙwace kadarorin, wannan hukuncin ba yana nufin an samu Malami da laifin aikata wani laifi ba.
A halin yanzu, Malami da matarsa da ɗansa na fuskantar wata shari'a ta daban kan zargin halasta kuɗaɗen haram da suka kai Naira biliyan 8.7, inda ake ci gaba da sauraron shari'ar a kotu.
Kotu ta kwace kadarori 57
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa, babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba da umarnin wucin gadi na kwace wasu kadarori da ake zargin na Abubakar Malami ne.
Mai shari'a Emeka Nwite ya ba da wa'adin kwanaki 14 ga duk wanda ke da hujjar mallakar dukiyoyin kafin kwace kadarorin gaba daya.
Wannan na zuwa ke bayan kotun ta ba da belin Malami da sauran wadanda ake tuhuma kan Naira biliyan 1.5 da sharudda masu tsauri.
Asali: Legit.ng

