Bayan Umarnin Kotu, An Kama Shugaban Hukumar Bogi da Ake Ta Cece Kuce a Kanta a Najeriya
- Dakarun 'yan sanda sun kama Adeniyi Adeyemi, shugaban hukumar bogi da ake ta ce-ce,-ku-ce kanta, a jihar Osun bayan umarnin kotu
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da sammacin kama shi bayan ya gaza gurfana a gabanta domin amsa tuhume-tuhumen da aka shigar a kansa
- Lauyan gwamnati ya ce Adeyemi ya ki halartar kotu sau biyar a jere, lamarin da ya alkalin ya ba da umarnin cafke shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Yan sanda sun kama Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin cewa shi ne shugaban hukumar bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).
Kama Adeyemi ya zo ne sa'o'i kadan bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin cafke shi saboda rashin halartar zaman kotu.

Source: Facebook
Wani mai amfani da kafar sada zumunta ta X, Imran Muhammad ne ya wallafa labarin kama Adeyemi, ya ce dakarun 'yan sandan sun cafke shi ne a jihar Osun.
Kotu ta bayar da sammacin kama shi
Mai shari'a Mohammed Umar ne ya bayar da sammacin kama Adeyemi bayan lauyan 'yan sanda kuma mai gabatar da kara, Wisdom Madaki, ya bukaci kotun da ta dauki wannan mataki.
An shirya gurfanar da Adeyemi domin ya amsa tuhume-tuhume takwas da suka shafi jabun takardu, damfara da kuma bayyana kansa da mukamin da ba a nada shi a hukumance ba.
Rundunar 'yan sanda ta shigar da karar ne da lamba FHC/ABJ/CR/562/2025 a Babbar Kotun Tarayya da ke yankin Maitama a Abuja.
Wanda ake zargin bai halarci kotu ba
Duk da cewa an saka karar a matsayi ta 12 cikin jerin shari'un ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026, Adeyemi bai bayyana a kotu domin amsa tuhume-tuhumen da ake masa ba.
Sai dai wani lauya mai suna Genesis Francis ya bayyana cewa yana wakiltar wanda ake zargin.
Lauyan gwamnati ya koka
Bayan an kira karar, lauyan gwamnati ya shaida wa kotu cewa Adeyemi ya ci gaba da kin halartar zaman shari'ar duk da damar da aka ba shi.

Kara karanta wannan
PFIPC: Kamfanin Amurka ya kawo ɗauki ga shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a Najeriya
Ya ce:
"Mai girma kotu, wannan ne karo na biyar da aka kawo wannan shari'a, kuma duk ɗagewar da aka yi saboda wanda ake kara ne."

Source: Twitter
Saboda haka, lauyan gwamnati ya bukaci kotun ta bayar da sammacin kama Adeyemi bisa tanadin Sashe na 394 na Dokar Gudanar da Shari'ar Laifuka (ACJA) ta shekarar 2015.
Leadership ta ce kotun ta amince da bukatar, inda ta bayar da umarnin a kama Adeyemi domin ya gurfana a gabanta, kuma sa'o'i kadan bayana haka yan sanda suka kama shi a Osun.
Kamfanin Amurka zai taimaki Adeyemi
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin Von Batten-Montague-York ya bayyana cewa a shirye yake ya taimaka wa Adeniyi Adeyemi wajen neman mafaka a Amurka.
Kamfanin ya ce duk da babu wata doka da ta kafa PFIPC, amma yadda ta gudanar da ayyukanta ya nuna akwai alamar cewa Adeyamj da ake zargi, yana da gaskiya.
Ya ƙara da cewa ya riga ya sanar da wasu manyan jami'an tawagar Shugaban Amurka Donald Trump game da lamarin hukumar PFIPC da ake zargin an kafa ba tare da izini ba.
Asali: Legit.ng
