Peter Obi Ya Bayyana Yiwuwar Haƙura da Neman Takarar Shugaban Kasa, Ya Kawo Dalili

Peter Obi Ya Bayyana Yiwuwar Haƙura da Neman Takarar Shugaban Kasa, Ya Kawo Dalili

  • Ɗan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi ya ce akwai yiwuwar ba zai sake neman takarar shugaban kasa ba bayan zaben 2027
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya danganta hakan da tsarin karba-karba na mulkin Najeriya tsakanin Arewa da Kudu
  • Obi ya ce idan mulki ya koma Arewa a 2031, zai kai shekara 78 kafin damar ta sake dawowa Kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ba zai sake neman kujerar shugaban kasa ba bayan babban zaben 2027.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce yiwuwar tsayawa takara a zaben 2031 ba ta da yawa, saboda tsarin karba-karba na shugabancin kasa tsakanin Arewa da Kudu da ake bi a siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027

Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Obi ya bayyana haka ne yayin wata hira da fitaccen dan jarida, Rufai Oseni, inda ya yi bayani kan makomarsa ta siyasa bayan zaben 2027.

Peter Obi ya fara hango bayan zaben 2027

Da aka tambaye shi ko zai sake neman takarar shugaban kasa idan bai yi nasara a 2027 ba, Obi ya ce matsayarsa za ta dogara ne da sakamakon zaben da kuma yadda za a tsara kujerun mulki kafin zaben 2031.

Ya ce:

"A gare ni, komai zai dogara da abin da zai faru a zabe na gaba. Ba na son in yi magana sosai saboda kada mutane su dauka ina nufin wasu ne."

Obi ya tuna tambayar wani dalibi

Peter Obi ya ce wani dalibin makarantar sakandare ya taba tambayarsa ko zai sake tsayawa takarar shugaban kasa bayan zaben 2027.

Ya ce ya amsa masa da cewa:

"Na ce masa idan ban tsaya takara yanzu ba, damar neman mulki za ta jima ba ta sake zuwa ba, idan aka bi tsarin karba-karba, mulki zai koma Arewa."

Kara karanta wannan

Jirgin sama ɗauke da mataimakiyar shugaban ƙasa da wasu mutum 8 ya yi hatsari

Obi ya bayyana cewa idan shugaban kasa daga Arewa ya hau mulki a 2031, lokacin da damar za ta sake komawa Kudu zai kai shekaru 78.

Mw zai sa Obi ya hakura da takara

A cewarsa:

"Idan mulki ya koma Arewa a 2031, lokacin da zai sake dawowa Kudu zan kai shekara 78, kuma ban ga zan ci gaba da wannan fafutuka a wannan shekarun ba."
Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa, Peter Obi yana jawabi a taron yan Obidient Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Sai dai tsohon gwamnan ya ce idan har mulki ya ci gaba da kasancewa a Kudu a 2031, akwai yiwuwar ya sake yin tunanin tsayawa takara, kamar yadda Leadership ta kawo.

"Idan har mulki ya ci gaba da kasancewa a Kudu a zabe na gaba, watakila. Amma yiwuwar hakan ba ta da yawa. Ba zan iya tabbatar da komai ba sai bayan sakamakon zaben 2027."

- Peter Obi.

Peter Obi ya yi hasashen mutuwa kafin 2027

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi , ya ce akwai yiwuwar ba zai kai lokacin zaben 2027 mai zuwa ba.

Peter Obi ya bayyana cewa wataƙila ba zai kasance a raye ba balle ya fafata a zaben na shekarar 2027, yana mai zargin gwamnatin trayya da muzgunawa yan adawa.

Peter Obi ya kuma yi zargin cewa gwamnati ta taso 'yan adawa a gaba inda ya bada labarin wani abu da ya taba faruwa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262