Ningi Ya Fadi Babbar Barazanar da Yake Fuskanta Bayan Dakatar da Shi a Majalisa

Ningi Ya Fadi Babbar Barazanar da Yake Fuskanta Bayan Dakatar da Shi a Majalisa

  • Dakataccen Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Sanata Abdul Ningi ya yi zargin cewa majalisar dattawa na shirin cafke shi
  • Ningi ya ce majalisar na shirin kama shi ne don tsuke bakinsa ta yadda ba zai iya yin komai ba kan zargin cushen N3.7tr a kasafin kuɗi da ya yi
  • Sanatan ya koka kan yadda ƴan majalisar suka ƙi sauraron zargin da ya yi inda suka mayar da hankali wajen ganin an kulle bakinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Sanata Abdul Ningi ya yi zargin cewa majalisar dattijawa na yunƙurin cafke shi kan zargin da ya yi na yin cushen N3.7tr a kasafin kuɗin shekarar 2024.

Abdul Ningi ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Tinubu na bada tallafin N500,000 ga matasa? Gaskiya ta bayyana

Ana kokarin cafke Sanata Ningi
Sanata Ningi ya yi zargin cewa majalisa na yunkurin cafke shi Hoto: @kc_journalist
Asali: Twitter

Abdul Ningi ya baro aiki a Majalisa

Idan ba ku manta ba dai majalisar dattawa ta dakatar da Ningi na tsawon watanni uku saboda iƙirarin da ya yi na cewa babu cikakken bayani kan yadda za a kashe Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kuɗin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ningi, ya riga da ya yi fallasar da babu wanda ya isa ya sauya mata fuska, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Wace barazana Ningi ke fuskanta a Majalisa?

A kalamansa:

"Wannan ne dalilin da ya sanya na ce na san majalisar nan ciki da waje, na daɗe a cikinta. Shiyasa muke magana. A bari mu yi magana.
"Shin sun tambayeni tun farkon wannan damɓarwar, ina bayanai na suke? Ina takardun suke? Ba tsayawa kawai na yi na ƙirƙiro lambobin ba.
"Babu wanda ya yi mani magana a kan hujja. Babu wanda ya nemi a saurareni. Abin da kawai suke ƙoƙarin yi shi ne tabbatar da cewa an tsuke bakin Ningi ko cafke shi ta yadda ba zai iya yin komai ba.

Kara karanta wannan

"Na karbi N266m": Abaribe, Ndume sun magantu kan ikirarin Ningi na cushe a kasafin 2024

"Na riga da na yi fallasa, ko su ko ni ba wanda ke da iko kan abin da hakan zai jawo.

Gidan talabijin na Arise Tv ya kawo rahoto cewa Sanata Jimoh Ibrahim ya buƙaci sufeto janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun da ya cafke Ningi kan zargin cushen da ya yi a kasafin kuɗin 2024.

Ningi: BudgIT ta tona gaskiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar da ke sa ido kan kasafin kuɗin Najeriya (BudgIT) ta goyi bayan Sanata Ningi kan zargin yin cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024.

BudgIT ta yi nuni da cewa a cikin kasafin kuɗin, babu cikakken bayani kan ayyuakan da za a gudanar da tsabar kuɗi har N3.7tr.

Asali: Legit.ng

Online view pixel