Sanata a ADC Ya Bukaci Atiku Ya Hakura da Takara a 2027, Ya Kawo Dalili

Sanata a ADC Ya Bukaci Atiku Ya Hakura da Takara a 2027, Ya Kawo Dalili

  • Jigo a jam'iyyar ADC, Sanata Victor Umeh, ya mika kokon bararsa ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
  • Sanata Victor Umeh ya sanar da Atiku Abubakar cewa ya kamata ya hakura da takara a zaben shekarar 2027
  • Victor Umeh wanda yake wakiltar mazabar Anambra ta Tsakiya ya bukaci Atiku ya kasance mai horar da shugabanni masu tasowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanatan da ke wakiltar mazabar, Anambra ta Tsakiya, Victor Umeh, ya aika sako ga Atiku Abubakar.

Sanata Victor Umeh ya ce ya kamata Atiku Abubakar ya yi la’akari da janyewa matasa ‘yan siyasa gabanin zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Victor Umeh ya ba Atiku shawara
Sanata Victor Umeh da Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Ohadimike tv, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Sanata Victor Umeh ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin ‘Prime Time’, na tashar Arise tv a ranar Litinin, 20 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Jonathan ya yi martani mai zafi bayan Atiku ya soki gwamnatinsa

Atiku zai hakura da takara bayan 2027

A makon da ya gabata, Abubakar ya bayyana cewa babban zaɓen 2027 zai kasance yunƙurinsa na ƙarshe na neman shugabancin ƙasa.

Ya ƙara da cewa matasan Najeriya masu neman mulki ya kamata su koyi dabarun jagoranci daga hannun tsofaffin shugabanni kuma su fara samun ƙwarewa.

Wace shawara sanata ya ba Atiku?

Sanata Victor Umeh wanda jigo ne a jam'iyyar ADC ya ce yana sa ran ganin tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai fara horar da sabon jini na shugabanni.

“Ina tunanin zai kasance a matakin da zai yi la’akari da barin fagen ga matasa, amma ya ce tsayawa takara zai yi."
“Don haka yana nufin duk abin da kowa ya faɗa a cikin watannin da suka gabata bai ratsa shi ba.”
“Kuma idan ya dage a kan cewa ba zai iya gina matasa su gaje shi ba don su sanya shi ya zama uba, to hakan yana nufin babu wanda ya shirya bayar da kofa ko kaɗan.”

Kara karanta wannan

"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027

- Sanata Victor Umeh

Sanatan ADC ya hango matsala

Sanatan ya ce burin Abubakar na neman mulki akai-akai zai iya jefa jam’iyyar ADC cikin haɗari.

“Tun shekarar 2003 yake takara. Muna girmama shi, babban ɗan siyasa ne mai faɗa a ji. Amma akwai lokacin da ya kamata ka ce, ‘Na yi, bari na taimakawa wasu su tashi."

- Sanata Victor Umeh

Legit Hausa ta tabbatar da cewa Atiku Abubakar bai yi takara a 2003 ba, ya dai nemi tikiti tun a zaben 1993 da 2015 kuma ya tsaya takara a 2007, 2019 da 2023.

Victor Umeh ya aika sako ga Atiku Abubakar
Sanata Victor Umeh a wajen taron jin ra'ayin jama'a kan dokar zabe ta 2026 Hoto: Ohadimike Tv
Source: Facebook

Sanata Victor Umeh ya yi gargadi

Sanata Umeh ya yi gargaɗin cewa gasa a tsakanin manyan jiga-jigan adawa na iya raunana ƙoƙarin gina dandali mai ƙarfi da zai iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki.

“Idan suka fita duka domin yin kokawa, za ta iya kai wa matsayin da wasu za su ji rauni a ƙarshe, kuma abin da zai wahala shi ne jam’iyyar, sannan wannan ƙoƙari na kawo dandali mai ƙarfi da zai fafata a zaɓe da jam’iyya mai mulki ba zai yi ma’ana ba."

Kara karanta wannan

"Najeriya ta yi rashi," Tinubu ya yi magana mai ratsa zuciya da Galadima ya mutu

- Sanata Victor Umeh

Ya kuma yi gargaɗin cewa irin wannan adawa na iya haifar da rarrabuwar kawuna da za su raunana haɗin kan ‘yan adawa gabanin zaɓubbukan.

Jonathan ya yi wa Atiku martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi Atiku Abubakar martani kan sukar da ya yi masa.

Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ya yi iya bakin kokarinsa lokacin da yake rike da madafun iko na kasar nan.

Jonathan ya ce babu wanda zai zama gwamna ko shugaban ƙasa da zai ce bai aikata wani kuskure ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng