Batun Takarar Kwankwaso da Obi Na Kara Karfi, an Kafa Sabuwar Kungiya
- Magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun kaddamar sa sabuwar kungiya ta siyasa
- Sabuwar kungiyar an kaddamar da ita ne gabanin fara zaben fidda gwani na masu neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC
- An kaddamar da kungiyar ne domin neman magoya baya kan takarar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Magoya bayan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, sun ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiyar siyasa, wato Obi-Kwankwaso (OK) Movement.
An kafa kungiyar ne yayin da ake ƙara kulla ƙawancen siyasa gabanin zaɓen tsaida gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC don babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce kungiyar, wadda ta sanar da bayyanarta a Abuja ranar Litinin, 20 ga watan Afirilun 2026 ta ce tuni ta kafa rassa a dukkan jihohi 36 na ƙasar nan da da kuma babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan
Abubuwan da 'yan Najeriya za su gani idan jam'iyyar ADC ta kifar da Tinubu a zaben 2027
An nada jagororin kungiyar OK
Hakazalika kungiyar ta naɗa masu gudanarwa na jihohi da shiyyoyi don gudanar da gangamin neman magoya baya.
Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar, Justin Ijeh, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Ya kwatanta wannan yunƙuri a matsayin haɗakar dakarun siyasa da suka haɗa da tafiyar Obidient Movement, Kwankwasiyya Movement, jam’iyyar NNPP, da kuma ADC.
Tafiyar ta OK Movement tana kama da tsari da kuma jan hankalin jama'a na tafiyar Obidient Movement, wadda gangamin matasa ya jagoranta kuma ya sauya fasalin siyasar Najeriya a lokacin zaɓukan 2023.
Meyasa aka kafa kungiyar Obi da Kwankwaso?
Yayin da yake jawabi ga manema labarai, Justin Ijeh ya ce dandali ne da ya haɗa mambobi daga Kwankwasiyya, Obidients, NNPP da kuma ADC, jaridar The Punch ta kawo labarin.
"A yau, yayin da mutanenmu ke fuskantar nauyin matsin tattalin arziƙi da ba a taɓa gani ba, tsadar rayuwa, da kuma matsalar rashin tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, ƙungiyar Obi-Kwankwaso (OK) Movement tana ƙaddamar da tsarinta na ƙasa da na jihohi a hukumance."
“Wannan ya wuce matakin siyasa kawai; bullar wani tsari ne na ƙasa baki ɗaya da aka tsara domin yin garambawul ga tsarin mulki da farfaɗo da ƙasa."
"Mun fahimci gajiyar da ake ji a kowane gida a Najeriya. Duk da haka, a cikin wannan lokaci na duhu, OK Movement tana tsaye a matsayin haske mai ƙarfi."
“Wannan tafiya gida ne ga dukkan ’yan Najeriya masu kyakkyawar manufa. Mun yi watsi da siyasar ƙabilanci, bangaranci, da ra'ayin addini waɗanda aka daɗe ana amfani da su wajen raba kan mutanenmu yayin da ƙasar ke tangal-tangal.”
- Justin Ijeh

Source: Facebook
Nafiu Bala ya yi zarge-zarge kan Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban tsagin jam'iyyar ADC na kasa, Nafiu Bala, ya yi zarge-zarge kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Nafiu Bala ya zargi madugun na Kwankwasiyya da cin amanar Arewa gabanin zaɓuɓɓukan shekarar 2023.
Ya bayyana cewa da shi da wasu masu ruwa da tsaki sun roki Kwankwaso ya marawa Atiku Abubakar baya domin kada a raba kuri'iun Arewa, amma ya ki yarda.
Asali: Legit.ng
