Abubuwan da aka Gani a Dakin Kabarin Annabi SAW da aka Shiga

Abubuwan da aka Gani a Dakin Kabarin Annabi SAW da aka Shiga

  • Wasu shugabannin ƙasashe da sarakunan Saudiyya sun samu damar shiga ɗakin da ake birne Manzon Allah (SAW) a Masallacinsa da ke Madina
  • Daga cikinsu akwai shugabannin Pakistan, Chechnya da Iran, waɗanda hukumomin harami suka tabbatar da cewa an taɓa buɗe musu ɗakin mai alfarma
  • A cikin ɗakin ƙabarin Manzon Allah (SAW) akwai kuma ƙaburburan Sahabbansa biyu, Abubakar As-Siddiq da Umar bn Khattab (RA)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Madina – Ɗakin da ƙabarin Manzon Allah Muhammad (SAW) yake a Masallacin Annabawi ya kasance wuri mai matuƙar daraja ga Musulmi, kuma ba kasafai ake buɗe shi ga jama'a ba.

Ƙabarin Manzon Allah (SAW) yana cikin ɗakin Nana Aisha (RA), wanda ke cikin Masallacin Annabawi, inda kuma aka birne Abubakar As-Siddiq da Umar bn Khattab (RA).

Kara karanta wannan

'Don Allah, a bari mu sarara': Kwankwaso ya 'gano' shirin Tinubu kan zaben 2027

Kabarin Annabi SAW
Wajen shiga dakin kabarin Annabi SAW a Madina. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Manyan Pakistan sun shiga dakin

BBC ta wallafa cewa hukumomin kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya, sun bayyana cewa an taɓa buɗe ɗakin ƙabarin Manzon Allah (SAW) ga wasu shugabanni.

Daga cikinsu akwai tsohon Firaministan Pakistan, Muhammad Nawaz Sharif, wanda ya sha ziyartar Masallacin Annabawi a Madina.

Haramain Sharifain ya kuma ce an taɓa buɗe ɗakin ga tsohon Firaministan Pakistan, Zulfikar Ali Bhutto, wanda ya mulki ƙasar daga 1973 zuwa 1977.

Haka kuma an buɗe ɗakin ga Janar Muhammad Zia-ul-Haq, wanda ya karɓi mulkin Pakistan bayan hambarar da gwamnatin Bhutto a shekarar 1977.

Ramzan Kadyrov ya shiga ɗakin

Hukumomin Haramain Sharifain sun ce shugaban Jamhuriyar Chechnya, Ramzan Kadyrov, yana cikin shugabannin da aka taɓa buɗe wa ɗakin ƙabarin Manzon Allah (SAW).

Kadyrov ya ziyarci Masallacin Annabawi a Madina a shekarar 2018, inda ya samu tarba daga hukumomin Saudiyya.

Ya zama shugaban Chechnya a shekarar 2007, bayan rasuwar mahaifinsa, Akhmad Kadyrov, wanda aka kashe a shekarar 2004.

Kara karanta wannan

Kwana 3 kafin zabe, INEC ta ƙara sunan ɗan takara 1 a zaben gwamnan jihar Osun

Masallacin Annabi SAW
Yadda masallacin Annabi SAW ya ke a Madina. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban Iran ya shiga dakin

Tsohon shugaban Iran, Sayyid Mohammad Khatami, shi ma yana cikin shugabannin da hukumomin Saudiyya suka ce an ba damar shiga ɗakin ƙabarin Manzon Allah (SAW).

Khatami ya kasance shugaban Iran daga 1997 zuwa 2005, kuma ya yi ƙoƙarin inganta alaƙa tsakanin Iran da ƙasashen Larabawa.

A shekarar 1998, ya ziyarci Saudiyya a wani rangadin da ya kai wasu ƙasashen yankin, inda ya gudanar da aikin Umrah a zamanin Sarki Fahd.

Ziyarar tasa ita ce ta farko da wani babban jami'in gwamnatin Iran ya kai Saudiyya tun bayan juyin juya halin Iran na shekarar 1979.

Sarakunan Saudi sun shiga dakin

Haramain Sharifain ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin sarakunan Saudiyya sun samu damar shiga ɗakin da aka birne Manzon Allah (SAW).

Hukumomin sun ce Sarki Abdulaziz da Sarki Faisal suna cikin sarakunan da aka rubuta a kundin tarihi cewa sun shiga ɗakin mai alfarma.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya tona yadda yan siyasa ke gwara yan Najeriya da sunan addini

Sai dai hukumomin sun ce akwai wasu sarakunan Saudiyya da suka kai ziyara ɗakin amma ba a samu rubuce-rubucen tarihi da suka tabbatar da hakan ba.

Abin da aka gani a cikin dakin

Sheikh Aaeed Ben Omar Al-Rouis, wani malamin Saudiyya, yana cikin mutanen da suka samu damar shiga ɗakin ƙabarin Manzon Allah (SAW).

Malamin ya ba da labarin ziyarar da ya kai ɗakin a lokacin da ya raka Sarki Faisal bin Abdulaziz, wanda ya mulki Saudiyya daga 1964 zuwa 1975.

Al-Rouis ya ce lokacin da suka shiga ɗakin, Sarki Faisal ya ga wasu akwatunan ƙarfe da ba a san abin da ke cikinsu ba.

Ya ce bayan kammala ziyarar, Sarki Faisal ya kafa wani kwamiti domin binciken abubuwan da ke cikin akwatunan.

An samu zinare da sauransu

Al-Rouis ya ce a lokacin yana wakiltar Ma'aikatar Kuɗi ta Saudiyya, kuma bayan an buɗe akwatunan, an samu zinare da wasu kayan ado a cikin ɗaya daga cikinsu.

Ya ce akwatin na biyu ya ƙunshi wasu sarƙoƙin azurfa, yayin da aka kuma samu wasiƙu daga Musulmi masu ɗauke da baitocin yabo da addu'o'i ga Manzon Allah (SAW).

Kara karanta wannan

Sabon rashin mutunci: 'Yan bindiga sun kakaba wa manomi haraji kafin girbi

Malamin ya ce damar shiga ɗakin ta ba shi damar ganin ƙabarin Manzon Allah (SAW), ƙaburburan Sahabbansa da kuma iyakokin ɗakin mai alfarma.

Sheikh Aliyu Ladan ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito rasuwar Sheikh Imam Aliyu Ladan, inda Dr Abdullahi Lamido ya bayyana marigayin a matsayin ɗan uwansa kuma malaminsa.

Dr Abdullahi Lamido ya ce Sheikh Aliyu Ladan ya kasance malami da Allah ya ba wa Alƙur'ani, sannan ya yi karatun Hadisi a Jami'ar Musulunci ta Madina.

Sulaiman Lawal Sule da wasu malamai da ɗaliban Riyadhul Qur'an sun bayyana alhini tare da roƙon Allah Ya gafarta wa Sheikh Aliyu Ladan, Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makomarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng