Kamar Buhari, an Fara Tarawa Pantami Miliyoyin Kudin Fom din Takara

Kamar Buhari, an Fara Tarawa Pantami Miliyoyin Kudin Fom din Takara

  • Magoya bayan Sheikh Is Ali Pantami sun fara gangamin tara masa kudin fom din takarar gwamna a jihar Gombe karkahsin jam'iyyar APC
  • Hakan na zuwa ne yayin da manufar tsohon ministan ta neman gwamna a jihar Gombe a zaben shekarar 2027 ke kara bayyana
  • Zuwa lokacin hada wannan rahoton, Legit Hausa ta gano cewa mutane da dama sun bayar da gudunmuwar miliyoyin Naira ga Pantami

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Masu goyon bayan tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami sun fara gangamin hada miliyoyin Naira domin saya masa fom din takara a 2027.

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sanar da cewa kudin fom din takarar gwamna zai kasance a kan Naira miliyan 50, kudin da ake shirin hadawa Pantami.

Kara karanta wannan

Jerin mutanen da Pantami zai gwabza da su a neman tikitin gwamnan APC a Gombe

Sheikh Pantami yayin sabunta katin APC
Lokacin da Isa Ali Pantami ke sabunta katin APC a Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Twitter

An fara hadawa Pantami kudin fom

Wani daga cikin na kusa da tsohon ministan, Abba Sani Pantami ya wallafa a Facebook cewa ya bude asusun kudin fom din da Naira miliyan 3.

Ya wallafa cewa:

"Ni Abba Sani Pantami na fara bada gudunmuwar Naira miliyan 3 a aljihuna don sayawa maigidanmu, Farfesa Isa Ali Pantami fom din tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe, wanda tuni na tura kudin."

Game da dalilin fara tara kudin fom din, Abba Pantami ya ce:

"Matasan da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami CON ya yi silar taimakon rayuwarsu da sauran masoyan shi sun kudiri aniyar saya masa fom din tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe da yardar Allah na kimamin Naira miliyan 50."

Ya kara da cewa:

"Tun a watannin baya matasan da maigidanmu Farfesa Isa Ali Pantami ya yi silar taimakon rayuwarsu suke ta kiran waya da a basu dama su tarawa mai girma, Majidadin Daular Usmaniyya kudi don su saya mishi form din takarar Gwamnan jihar Gombe a zabe mai zuwa, wanda jam'iyyar APC ta fitar za ta fara sayarwa a mako mai zuwa a kan kimamin Naira miliyan 50."

Kara karanta wannan

Arewa da Kudu za su amfana da Tinubu ya nemi izinin sake ciyo bashin Dala miliyan 516

Kwamitin tarawa Pantami kudin fom

Abba Pantami ya bayyana cewa wannan dalilin yasa matasan suka kafa kwamiti da zai jagoranci sayawa Pantami fom din karkashin jagorancin Muhammad Sani Ado Hausawa

Ya kara da cewa kwamitin ya tsara duk wanda yake da niyya ya shirya ya tura kudin ta asusun shugaban kwamitin da aka riga aka bayar.

A bisa jerin sakonnin da Ado Hausawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, Legit ta gano cewa mutane da dama sun tura makudan kudi ta asusun bankin.

Sheikh Isa Ali Pantami
Isa Ali Pantami yayin wa'azi a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a tantance adadin kudin da aka tara ba, sai dai ana tsammanin kwamitin zai fitar da rahoto daga baya.

Abokan neman takarar Pantami

A wani rahoton, mun kawo muku cewa Sheikh Isa Ali Pantami zai buga takarar neman tikitin gwamna a jam'iyyar APC a jihar Gombe da mutane 11.

Abokan takarar shi sun hada da gogaggun 'yan siyasa kamar Jamilu Isiyaku Gwamna, Sanata Saidu Ahmed Alkali da Hon. Usman Bello Kumo.

Sauran sun hada da 'yan kasuwa, kwararrun ma'aikatan gwamnati kamar Alhaji Yunusu Yakubu, Alhaji Umaru Kwariga da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng