Rigima Ta Barke tsakanin Matasan Gari da Fulani Makiyaya, Mutum 3 Sun Bakunci Lahira
- Mutane uku sun mutu sakamakon arangama tsakanin fulani makiyaya da matasan kauyen Mwaghavul da ke Mangu a jihar Filato
- Daya daga cikin wadanda suka mutu dan yankin ne, yayin da biyu makiyaya ne da aka yi rigimar da su
- Sojoji sun shiga tsakani tare da gudanar da samame da amfani da jiragen sama marasa matuki domin tabbatar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Mutane uku sun rasa rayukansu sakamakon arangama tsakanin makiyaya da matasan garin Mwaghavul a Jwak Maitumbi da ke karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Bayan rasa rayukan mutum uku a rikicin, bayanai sun nuna wani mutum daya daga cikin al’ummar garin ya samu raunuka.

Source: Original
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa daya daga cikin wadanda suka mutu dan garin Mwaghavul ne, yayin da aka kashe makiyaya 2.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya maida hankali kan samar da ayyuka masu gwaɓi ga matasan Najeriya
Rikicin ya barke da matasa a Filato
Rahoton ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:35 na safe ranar 12 ga Agusta, bayan wata arangama da ta faru tun farko tsakanin matasan al’ummomin biyu.
Sojoji sun shiga tsakani bayan samun rahotannin cewa ana ci gaba da jin karar harbe-harbe a yankin.
Rahoton ya nakalto cewa:
“Sojojin sun mayar da martani kan rahotannin ci gaba da harbe-harbe a wurin, inda suka garzaya domin shawo kan lamarin.”
Sojoji sun tilasta musu ja da baya
Rahoton ya ce sojojin sun yi amfani da karfin da ya fi na bangarorin rikicin, lamarin da ya tilasta wa bangarorin biyu janyewa daga yankin.
Daga bisani sojojin sun gudanar da sintirin tabbatar da tsaro tare da amfani da sa ido ta jiragen sama marasa matuki, wanda ya tabbatar da cewa babu sauran mayakan da ke yankin.
An dawo da zaman lafiya
Rahoton ya ce sojojin sun ci gaba da mamaye yankin domin hana sake barkewar tashin hankali da kuma dakile duk wani yunkurin bangarorin rikicin na sake taruwa.
Jami’an tsaro sun kuma ci gaba da sanya ido a yankunan da abin ya shafa yayin da ake daukar matakan hana rikicin kara kamari, kamar yadda The Cable ta kawo.

Source: Twitter
Rikicin manoma da makiyaya ya shafe shekaru da dama yana haddasa asarar rayuka da raba dubban mutane da matsugunansu a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa yankin Arewa ta Tsakiya na daga cikin wuraren da wannan rikici ya fi yin kamari, inda jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da kokarin dakile tashin hankalin.
Dalilin ci gaba da rikici a Filato
A wani rahoton, mun kawo muku cewa tsohon gwamnan Filato, Jonah Jang, ya ce rikicin jihar ya samo asali ne daga matsalolin tarihi, siyasa, ƙasa, adalci da batun ‘yan asali da ‘yan ƙasa.
A cewar tsohon gwamnan, gazawar shugabannin jihar da rashin magance matsalolin da ke ƙasa tun farko sun taimaka wajen tsawaita rikicin.
Jang, wanda ya taɓa zama gwamnan mulkin soja na jihohin Benue da Gongola, ya zargi gwamnatocin da suka biyo baya da kasa ɗaukar matakan da suka dace wajen magance rikicin Filato.
Asali: Legit.ng
