Legas Ta Kafa Cibiyar Amfanin Gona yayin da ake Auren Gata a Arewa
- Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya buɗe sabuwar cibiyar kayan amfanin gona a Agege domin ƙara ƙarfafa tsarin samar da abinci a jihar
- Gwamnan ya ce cibiyar za ta taimaka wajen rage tsawon hanyoyin da kayan abinci ke bi kafin su isa kasuwanni da kuma rage asarar amfanin gona
- Sanwo-Olu ya ce samar da wadataccen abinci na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa saboda bunƙasar Legas tana da alaƙa da ingancin tsarin samar da abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Legas – Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya buɗe sabuwar cibiyar kayan amfanin gona mai matsakaicin mataki a Agege domin ƙara ƙarfafa samar da abinci a jihar.
Gwamna Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa ta sanya batun samar da wadataccen abinci a cikin manyan ajandun ci gaban jihar.

Source: Facebook
Dalilin kafa cibiyar a Legas
A sakon da ya wallafa a Facebook, Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta fara sake duba tsarin samar da abinci a jihar tun shekarar 2021.
Ya ce Legas na da yawan jama'a sama da miliyan 25, lamarin da ke haifar da babbar buƙatar abinci a kullum.
Sanwo-Olu ya ce sama da kashi 70 cikin 100 na abincin da ake amfani da shi a jihar ana samar da shi ne a wajen Legas.
Ya ce kayan abincin na yin doguwar tafiya ta hanyoyin samar da kayayyaki kafin su isa kasuwanni, abin da ke haifar da tsadar sufuri da asarar amfanin gona.
Za a rage asarar amfanin gona
The Cable ta wallafa cewa gwamnan ya ce kafa cibiyoyin da ya yi zai taimaka wajen rage tsawon hanyoyin samar da abinci.
Ya ce cibiyoyin za su rage yawan masu shiga tsakani, inganta yadda ake sarrafa kayan amfanin gona da kuma sauƙaƙa rarraba abinci zuwa kasuwanni.

Kara karanta wannan
Yajin aiki: Jerin jami'o'i 20 da ASUU ta fara shirin dakatar da harkokin karatu a Najeriya
Sanwo-Olu ya ce ba a samar da ƙarin abinci kaɗai ake buƙata kawai ba, ana son sauya tsarin daga noman amfanin gona zuwa tattarawa, sufuri, sarrafawa da kai shi kasuwa.
Shirye-shiryen bunƙasa aikin noma
Sanwo-Olu ya ce shirin karfafa manoma yana ƙara sha'awar aikin noma tsakanin ɗalibai a sama da makarantun sakandare 440 na jihar.
Ya ce shirin horas da masu fawa na horas da sababbin masu sana'ar yanka nama kan tsafta da hanyoyin sarrafa nama na zamani.

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma bayyana cewa masana'antar shinkafa ta Lagos da ke Imota, wadda ya ce ita ce mafi girma a Afirka, ta samar da buhunan shinkafar Eko sama da 250,000 masu nauyin kilogram 50 a shekarar da ta gabata.
Magana kan auren gata Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani bidiyo daga shirin auren gata da gwamnatin Kano ta shirya ya jawo ce-ce-ku-ce kan yadda ake kashe kuɗin gwamnati.
Rahoto ya nuna cewa wani ango ya bayyana farin cikinsa a wajen bikin inda ya ce zai iya kara wata mata idan ya samu dama a gaba.
Shirin auren na daga cikin wani shiri na gwamnatin jihar Kano da aka ware Naira biliyan 1.5 domin taimaka wa ma'aurata 1,500 su yi aure.
Asali: Legit.ng
