Da duminsa: Hukumar EFCC ta turke kwamishanan Ganduje, Murtala Garo, bisa mallakan wasu dukiyoyi

Da duminsa: Hukumar EFCC ta turke kwamishanan Ganduje, Murtala Garo, bisa mallakan wasu dukiyoyi

- Kwamishanan kananan hukumomi, Murtala Garo, na amsa tambayoyi hannun jami'an EFCC

- An bayyana cewa kwamishanan na amsa tambayoyi ne bisa mallakan wasu manyan dukiyoyi a Kano da Abuja

- Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da labarin cewa lallai an gayyaceshi

Wani rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa kwamishanan kananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Garo, na amsa tambayoyi hannun jami'an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.

A cewar rahoton, ana binciken kwamishanan ne bisa mallakan wasu manya dukiya a jihar Kano da birnin tarayya Abuja.

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar da hakan ga jaridar yayinda aka tambayeshi.

Amma ya ce gayyatan kwamishanan kawai aka yi ba garkameshi ba.

Ya ce an gayyaceshi ne don bayani kan wasu abubuwa.

Da duminsa: Hukumar EFCC ta turke kwamishanan Ganduje, Murtala Garo, bisa mallakan wasu dukiyoyi
Da duminsa: Hukumar EFCC ta turke kwamishanan Ganduje, Murtala Garo, bisa mallakan wasu dukiyoyi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda matashi dan shekara 22 ya nitse cikin kogi a Kano

Majiya ta bayyana cewa hukumar yaki da rashawan jihar Kano ta gayyaci kwamishanan yayi bayani kan dukiyokokin da ya mallaka na gidaje, motoci, gidajen mai, da sauransu.

Wannan ya biyo bayan yabawan da wata kungiya mai zaman kanta, Centre for Public Trust (CPT), ta yiwa gwamna Abdullahi Ganduje, bisa kafa kwalejin yaki da rashawa a jihar.

A wasikar ta aike masa, kungiyar ya taya gwamnan murna bisa abinda suka siffanta matsayin "matakin da ya dace wajen sauya tsarin mulki a jihar."

A bangare guda, Gwamnatin jihar Kano ta amince da bude cibiyoyin zana jarabawar JAMB a masarautu biyar na jihar da suka mamaye kananan hukumomi 44 na shiyyoyi 5 na jihar.

Kwamishinan watsa labarai, Malam Muhammadu Garba ya bayyana hakan jim kadan bayan fitowa daga taron majalisar zartaswa na jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.

"An yanke shawarar kara adadin cibiyoyin zana jarabawar ne la'akari da korafe korafen da al'ummar ke shigarwa, na tura daliban jihar zuwa jihohin Bauchi, Kaduna, Jigawa ko Katsina."

Mallam Garba ya kuma bayyana cewa a yayin wannan zaman, majalisar zartaswar ta amince da bude cibiyar jiha kan watsa labarai da sadarwa (ICT) domin yada ilimin ICT tun daga kauyuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel