Matan da aka Gani Sun Fito Neman Kujera a Zaben Gwamnan Osun

Matan da aka Gani Sun Fito Neman Kujera a Zaben Gwamnan Osun

A wannan takarar gwamnan jihar Osun, har yanzu mata na fuskantar babban kalubale wajen samun damar shiga fafutukar neman kujerar gwamna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun – Daga cikin ’yan takara 15 da suka shiga fafatawar neman kujerar gwamna, tun kafin janye takarar dan takarar APGA, Adesina Adeyemi-Doro, mace daya ce kacal ta fito takarar gwamna, yayin da daya kuma ke neman zama mataimakiyar gwamna.

Wannan karancin wakilcin mata ba sabon abu ba ne a zabukan Najeriya, inda a lokuta da dama ake samun ’yan takarar mata kalilan ko kuma babu ko daya.

An samu karancin mata a zaben Osun
Temi Tope Ogiri da Yemisi Adeagbo su ne matan da aka gani a zaben Osun Hoto: Osun Defender/ADP
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa tun bayan da gwamnatin mulkin soja karkashin Janar Ibrahim Babangida ta kirkiro Jihar Osun a shekarar 1991, dukkan gwamnonin da suka jagoranci jihar maza ne.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Jerin manyan yan takarar gwamna 14, jam'iyyu, shekaru da matakin karatunsu

Sai dai mata biyu sun taba lashe zabe tare da rike mukamin mataimakiyar gwamna a jihar. Su ne Olusola Obada, wadda ta rike mukamin daga 2003 zuwa 2010, da Titilayo Laoye-Tomori, wadda ta kasance mataimakiyar gwamna daga 2010 zuwa 2018.

Matan da suka fito takara a Osun

Duk da karancin matan da suka fito neman mukamai a babban zaben jihar Osun da ake gudanarwa a yau, akwai wadanda suka yi yunkurin shiga fafatawar.

1. Yemisi Adeagbo

Bisa bayanan da hukumar zabe ta wallafa, Yemisi Adeagbo, tsohuwar shugabar makaranta ce kuma ’yar takarar gwamna ta jam’iyyar ADP, yayin da Atanda Babatunde ya ke matsayin abokin takararta na mataimakin gwamna.

An samu mace mai neman takarar gwamna a Osun
Yar takarar gwamna a jihar Osun Yemisi Adegabo Hoto: ADP
Source: Facebook

Bayan sanar da takararta, Adeagbo ta bayyana cewa idan aka zabe ta, gwamnatinta za ta daga jihar daga matsayin da take yanzu zuwa matsayin jihar abin koyi da sauran jihohin tarayya za su duba domin koyi da kyakkyawan shugabanci.

Ta ce ADP ita ce jam’iyyar da ta fi mayar da hankali kan jama’a, wadda aka gina bisa ingantattun tsare-tsare, ba ta fama da rikicin cikin gida, kuma manufarta ita ce yi wa jama’a hidima ba biyan bukatar son kai ba.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan sani 11 kan jihar Osun yayin da ake gudanar da zaben gwamna

2. Temitope Agiri

A ruwayar The Sun, Temitope Agiri ta jam’iyyar ADC ce kadai daga cikin sauran ’yan takarar da ta shiga takarar mataimakiyar gwamna. Ita ce abokiyar takarar Najeem Salaam, tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun.

Temitope na neman kujerar mataimakin gwamna a Osun
Temitope Agiri, yar takarar mataimakin gwamnan Osun Hoto: Osun Defender
Source: Facebook

Jam’iyyar ta bayyana Agiri, wadda ta fito daga Ila-Orangun da ke karamar hukumar Ila, a matsayin wadda ta fi cancanta saboda biyayyarta ga jam’iyyar da kuma karbuwarta a tsakanin mambobin jam’iyyar a fadin jihar.

A cewar jam’iyyar, zabar Agiri, musamman saboda kasancewarta mace da kuma tarihinta na siyasar cikin gida, zai kara wa jam’iyyar damar samun nasara a zaben.

Ana samun karancin mata a zaben Osun

Rahoton ya ce a zaben gwamnan Osun na shekarar 2022, babu ko mace daya cikin ’yan takara 15 da suka fafata neman kujerar gwamna. Sai dai mata shida sun shiga takarar mataimakan gwamna.

A zaben watan Satumban 2018, wanda aka gudanar domin maye gurbin Rauf Aregbesola, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta amince da ’yan takara 48, ciki har da mata hudu.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya koma kan matatun mai bayan karɓar tawagar NUPENG

Matan da suka tsaya takarar sun hada da Adebisi Rufai ta jam’iyyar ACPN, Hannah Jegede ta NEPP, Mercy Ayodele ta RP) da Adebayo Rasheedat ta PANDEL. Har ila yau, a zaben na 2018 akwai akalla mata 16 da suka tsaya takarar mataimakan gwamna.

Yankunan da za su yi tasiri a Osun

A baya, kun samu labarin cewa zaben gwamnan Osun na ranar 15 ga Agusta, 2026 ya fi karkata kan Adeleke, Oyebamiji da Salaam, wadanda duk suka fito daga Osun ta Yamma Osogbo, Olorunda, Ife Central, Ife ta Gabas.

Ife ta Kudu, Odo Otin, Iwo da Ilesa ta Gabas na cikin manyan kananan hukumomin jihar Adeleke na dogaro da ayyukan raya kasa da karfin Ede, yayin da Oyebamiji da Salaam ke neman samun gagarumar nasara a wasu muhimman kananan hukumomi.

Adeleke da Salaam sun fito daga mazabar tarayya ta Ede ta Arewa, Ede ta Kudu, Egbedore da Ejigbo, yayin da Oyebamiji ya fito daga Irewole, Isokan da Ayedaade wadanda ke fafatwa da Ademola Adeleke da ke gudana/

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng