EFCC Ta Kai Wani Mutum Kotu kan Zargin Baba Kere da N56m na Kudin Aikin Hajji

EFCC Ta Kai Wani Mutum Kotu kan Zargin Baba Kere da N56m na Kudin Aikin Hajji

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da wani mutum a gaban babbar kotu bisa zargin damfarar N56.5m da aka tara domin aikin Hajjin 2023
  • Ana zargin ya karɓi kuɗin daga Ibrahim Shuaibu, bayan ya yi ikirarin cewa ma’aikacin gwamnatin Kaduna ne da zai taimaka wajen aikin Hajji
  • EFCC ta ce mutane 10 da ake kiwon shanu a Oke-Ogun sun ba da kuɗin, amma babu wanda ya je Saudiyya saboda Musa bai cika alkawarinsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Hukumar Yaƙi da Yiwa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da wani mutum kan zargin damfarar kudin aikin hajji.

Ana zargin mutumin mai suna Lawal Musa bisa zargin damfarar N56.4m da aka biya domin aikin Hajjin 2023.

EFCC ta kai wani kotu kan zargin damfarar kudin aikin hajj
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyode. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Source: UGC

Zargin da ake yi wa mutumin

An gurfanar da Musa ne a ranar Alhamis a gaban Babbar Kotun Oyo da ke Ibadan, inda ake tuhumarsa da tuhume-tuhume 57 da suka shafi karkatar da kuɗi, yin jabun takardu da amfani da takardun bogi, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Yadda aka kama fasto da ya kulla sace matan wasu malaman addini a Plateau

A cewar wata sanarwa da Dele Oyewale, shugaban yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na EFCC, ya fitar ranar Juma’a, Musa ya karɓi N56.5m da Ibrahim Shuaibu ya tara domin gudanar da aikin Hajjin mutane 10.

Hukumar EFCC ta ce Musa ya yi ikirarin cewa yana aiki da gwamnatin Kaduna kuma zai iya taimaka wa mutanen wajen samun damar zuwa aikin Hajjin 2023.

Mutanen da aka ce an tara kuɗin domin su ne Jibril Adamu, Suleiman Aminatu, Musa Haruna, Suleiman N. Abdullahi, Audu Bello, Yusuf Umaru, Saidu Musa, Idris Suleiman, Musa Yunusa da Usman Haruna.

Wani mutum ya shiga matsala kan taba kudin aikin hajji har N56m
Shugaban hukumar EFCC a Najeriya, Ola Olukayode da ofishin hukumar. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission.
Source: Facebook

Yadda Musa ya kirkiri takardun bogi

EFCC ta bayyana cewa waɗanda ake zargin an damfara ’yan kasuwar kiwon shanu ne da ke gudanar da harkokinsu a yankin Oke-Ogun na Oyo.

Hukumar ta kuma zargi Musa da ƙirƙirar takardun karɓar kuɗi na Hukumar Jin Daɗin Mahajjatan Kaduna, sannan ya gabatar da su a matsayin sahihai.

Kara karanta wannan

Maganin mallaka: Matashin da ya birne Kur’ani da wasu kayan tsubbu ya shigo hannu

Ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen ya ce Musa ya ƙirƙiri takardar karɓar kuɗi mai lamba 0013041 ta Hukumar Jin Daɗin Mahajjatan Kaduna da sunan Jibril Adamu, da nufin a ɗauke ta a matsayin takarda ta gaskiya.

Musa ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka karanta masa a gaban Mai Shari’a Olusola Adetujoye.

Bayan ya musanta laifukan, lauyan EFCC, Bashir Shamsudeen, ya nemi kotu ta sanya ranar fara shari’ar tare da umartar a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali.

Yadda ake zargin damfarar ta faru

EFCC ta ce lamarin ya fara ne lokacin da Musa ya je wajen Shuaibu, inda ya yi ikirarin cewa ma’aikacin gwamnatin Kaduna ne kuma zai iya shirya tafiyar mutane zuwa aikin Hajjin 2023.

Daga nan Shuaibu ya sanar da mutane 10 da ke kiwon shanu, kuma a cewar hukumar, waɗanda ake zargin an damfara sun tara kusan N56.5m.

Hukumar ta ce daga bisani aka tura kuɗin zuwa hannun Musa domin ya shirya tafiyar mutanen zuwa aikin Hajji.

Sai dai EFCC ta ce babu ko mutum ɗaya daga cikin mutanen 10 da ya samu damar zuwa Saudiyya domin aikin Hajjin 2023, saboda Musa bai cika alkawarin da ya yi musu ba.

Kara karanta wannan

Miyagu daga kabilar Tibi sun hallaka direban Dangote da wata mata a Benue

Kamfanonin da za su jigilar mahajjata a 2027

Kun ji cewa hukumar alhazan Najeriya (NAHCON) ta amince da kamfanonin jiragen sama 5 domin jigilar mahajjatan Najeriya a Hajjin 2027.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen aikin Hajjin badi, wanda NAHCON ke sa ran sauke nauyinta da wuri.

An ce kamfanonin za su cika ka’idojin tsaro da na hukumomin zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya da Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.