Dangote Ya Je Amurka, Ya Fadi Yadda ake Amfani da Karfi don Hana Afrika Cigaba
- Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya halarci wani muhimmin taron tattalin arziki da aka gudanar a birnin Washington DC na kasar Amurka
- Dan kasuwar ya bayyana wasu abubuwan da suke hana kawo cigaba a Afrika tare da dakile tattalin arzikin kasashen yankin da dama
- Dangote ya kuma yi magana game da muhimmancin 'yan Afrika su rika saka jari a yankunan su, domin a cewarsa hakan ne mafita a gare su
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Alhaji Aliko Dangote da ya kafa rukunin kamfanonin Dangote ya ce akwai wasu 'yan kasashen waje da ke hana ci gaban Afirka.
Baya ga haka, Dangote ya yi bayani game da wasu matakai da ya kamata 'yan Afrika su dauka idan suna son kawo cigaba mai dorewa a nahiyarsu.

Source: Getty Images
The Cable ta rahoto cewa Attajirin ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wajen taro kan tattalin Africa da aka gudanar a gefen taron IMF da Bankin Duniya a Washington, DC.
Magana kan kafa kasuwar Afrika
Aliko Dangote ya yi kira ga kan hadin gwiwar yankunan Afrika, inda ya ce da wahala a iya samar da kasuwa guda daya a nahiyar ba tare da tabbatar da kananan kasuwannin yankunan sun fara aiki yadda ya kamata ba.
“Yarjejeniyar kasuwanci ta Afirka za ta yi aiki, amma za ta yi ne kawai idan kananan kasuwannin yankuna sun yi aiki,”
In ji shi.
“Dole ne kananan kasuwannin yankuna su fara aiki kafin samar da babbar kasuwa daya, domin wadannan yankuna da ake da su a yanzu ba sa aiki yadda ya kamata.
Maganar hana Afrika cigaba
Yayin da yake bayani kan cigaban nahiyar, Dangote ya ce dole ne a san da cewa akwai wasu 'yan kasashen duniya da ba sa son ganin Afirka ta bunkasa.
Dangote ya ce Afirka ta gagara samar da sabuwar matatar mai lokaci mai tsawo, yana mai cewa akwai abubuwa da dama da ke hana samar matatar mai a wasu kasashe.
Maganar Dangote kan gina Afrika
Dangane da jawo masu zuba jari daga kasashen waje zuwa nahiyar, dan kasuwar ya jaddada cewa zuba jari daga waje na dogara ne da yadda ake kallon abubuwan da ke faruwa a cikin gida.

Source: Getty Images
Ledership ta rahoto ya ce dole ne ‘yan Afirka su fara zuba jari a kasashensu kafin masu zuba jari daga waje su zo:
“‘Yan kasashen waje za su zuba jari. Amma su ma mutane ne masu hankali. Duk inda aka ambaci cewa akwai matsala, za su yi nazari sosai.
“Idan ni ban zuba jari a Afirka ba, babu yadda zan iya shawo kan wani daga wajen nahiyar ya zo ya zuba jari.”
An san da tasirin Dangote a duniya
A wani labarin, mun kawo muku cewa an sanya Alhaji Aliko Dangote cikin manyan mutane 100 da suka fi tasiri a duniya a 2026.
Rahoto ya nuna cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump na cikin manyan mutanen da aka karrama tare da Aliko Dangote.
Dangote ne dan Najeriya daya tilo da ya samu shiga jerin manyan mutanen a wannan karon, sai dai akwai wasu 'yan Afrika a cikinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

