PDP Ta Kuma Babban Rashi, Tsohon Gwamnan Ondo Ya Sanar da Rabuwa da Jam'iyya

PDP Ta Kuma Babban Rashi, Tsohon Gwamnan Ondo Ya Sanar da Rabuwa da Jam'iyya

  • Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya sanar da ficewarsa daga babbar jam’iyyar adawa PDP
  • Ya ce ficewar ta fara aiki daga ranar 10 ga Afrilu, 2026 yayin da PDP ke ci gaba da rasa jiga-jiganta ga APC da ADC
  • Olusegun Mimiko ya bayyana cewa ya bayyana matsayarsa ne bayan tambayoyi da ake yi masa game da zama a PDP

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar ondo – Tsohon gwamnan jihar Ondo, Dokta Olusegun Mimiko, ya hakura da zama ɗan jam’iyyar PDP a hukumance, inda ya ce ya ɗauki wannan mataki ne domin saboda jama’a.

Mimiko, wanda ya mulki jihar Ondo tsakanin 2009 zuwa 2016, ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam’iyyar a mazabarsa ta Ward 7, a ƙaramar hukumar Ondo ta Yamma.

Kara karanta wannan

"Saura ƙiris": Trump ya faɗi lokacin kawo ƙarshen yaƙi da Iran

Mimiko ya sanar da barin PDP
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Mimiko Hoto: Akinrotoye Kehinde Bonsue
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin wasiƙar, ya ce, tuni ya mika takardar domin kwantar da hankulan jama'a da ke tambayarsa makomar siyasarsa.

Tsohon gwamnan Ondo ya bar PDP

Daily Post ta wallafa cewa barin PDP da Mimiko ya yi ta kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi a kan siyasarsa a Nijar Ondo.

A sakon da Olusegun Mimiko ya fitar, ya ce:

“Ina miƙa takardar fice wa daga jam’iyyar PDP, wanda zai fara aiki daga ranar 10 ga Afrilu, 2026.”

Ya ƙara da cewa jita-jita da tambayoyi da ake yi kan matsayin sa a jam’iyyar ne suka sa ya ga ya dace ya fito fili ya bayyana gaskiya.

“Saboda na ɗan nesanta kaina daga harkokin jam’iyya a baya-bayan nan, ina so a rubuce cewa ba ni da alaƙa da PDP a yanzu."

Matakin Mimiko bayan barin PDP

Mimiko ya jaddada cewa ya ɗauki wannan mataki ne ba tare da wata gaba ko saɓani da kowa a cikin jam’iyyar PDP ba.

Kara karanta wannan

Wutar rikici ta fara tashi a jam'iyyar APC, Yilwatda ya gargadi tsafaffin ƴan PDP

A baya-bayan nan, Mimiko ya kasance yana nesanta da siyasar jam’iyya, abin da ya haifar da rade-radin cewa wataƙila ya sauya sheƙa ko kuma yana shirin yin hakan.

Duk da haka, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance da ke nuna ko tsohon gwamnan zai shiga APC ko ADC.

Mimiko bai sanar da inda zai koma
Taswirar jihar Ondo inda siyasar jihar ke shirin canja salo Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa matakin da Mimiko ya ɗauka na iya zama wani shiri na komawa sahun gaba a siyasar ƙasa, musamman yayin da ake tunkarar zaɓukan gaba a Najeriya.

Ficewar tasa daga PDP na iya sauya wasu lissafin siyasa a jihar Ondo, ganin irin tasirin da yake da shi a yankin, duk da cewa ya jima bai fito fili yana taka rawa sosai a harkokin jam’iyya ba.

'Dan majalisar PDP ya sauya sheka

A baya, mun ruwaito cewa ɗan majalisar wakilai Abdussamad Dasuki na Kebbe/Tambuwal a jihar Sakkwato ya yi murabus daga jam’iyyar PDP.

AbdusSamad Dasuki ya sanar da komawarsa jam’iyyar hamayya ta ADC da ke kokarin karbe mulki a hannun APC a Najeriya a zaben shekarar 2027 mai zuwa

Kara karanta wannan

APC a Adamawa ta rikice, mai neman takarar gwamna ya fice daga jam'iyya

Ɗan majalisar ya ce matakin sauya shekarsa ya biyo bayan tuntuba da magoya bayansa kan yadda goben siyasarsa za ta kasance a Sakkwato da Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng