PDP ta yi babban kamu, tsohon Gwamna ya tattara daukacin ‘Yan jam’iyyarsa sun sauya-sheka

PDP ta yi babban kamu, tsohon Gwamna ya tattara daukacin ‘Yan jam’iyyarsa sun sauya-sheka

  • Dr. Olusegun Mimiko da magoya bayansa sun amince su sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP mai adawa
  • Tsohon gwamnan da sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar Zenith Labour Party da ke jihar Ondo, sun shiga PDP
  • Shugaban jam’iyyar ZLP na jihar Ondo, Joseph Akinlaja, ya bada wannan sanarwa a ranar Alhamis

Ondo - Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya dawo jam’iyyar PDP mai hamayya, bayan zama da gwamnonin da Aminu Tambuwal ya jagoranta.

Jaridar Vanguard tace Dr. Olusegun Mimiko ya fice daga jam’iyyar adawa ta Zenith Labour Party watau ZLP da ya kafa bayan ya sauya-sheka daf da zaben 2019.

The Nation tace a wani jawabi da shugaban jam’iyyar ZLP na reshen jihar Ondo, Hon Joseph Akinlaja, ya fitar a ranar Alhamis, an tabbatar da sauya-shekar.

Hon Joseph Akinlaja yace masu ruwa da tsaki a jam’iyyar hamayyar ta ZLP daga duka kananan hukumomi 18 da ke jihar Ondo, duk sun zabi su shiga jirgin PDP.

Mimiko da shugabannin ZLP sun yi zama

Wadanda suka halarci taron da aka yanke wannan hukunci sun hada da tsohon gwamna Mimiko, sai Agboola Ajayi, da abokin tafiyarsa, Gboye Adegbenro.

Tsohon shugaban majalisar dokoki na jihar Ondo, Rt. Hon. Jumoke Akindele ya halarci zaman.

Tsohon Gwamnan Ondo
Segun Mimiko yana Gwamna Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahoton yace Akinlaja da sauran manyan ZLP sun amince su sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP domin su ceto kasar nan daga mulkin da gwamnatin APC take yi.

‘Yan siyasar sun ji dadin yadda PDP ta nuna sha’awar ta tafi da su ta hanyar karkato da ra’ayin Mimiko wanda ya mulki jihar Ondo tsakanin shekarar 2009 da 2017.

“Zaman ya zo ne bayan wasu gwamnoni hudu na PDP a karkashin Aminu Tambuwal sun fadawa Mimiko suna zawarcinsa da sauran ‘ya ‘yan ZLP.”
“An kira taron masu ruwa da tsaki domin a tattauna game da taron da aka yi da gwamnonin PDP, ana aiko masa goron gayyata.” - Joseph Akinlaja.

Hakan yana nufin PDP ta yi nasara a kan jam'iyyar APC wajen dauke 'dan adawar, yayin da ake shirin 2023. Mimiko yana da mabiya da-dama a kudu maso yamma.

Zuwan Tambuwal ya yi amfani

A jiya Gwamnonin PDP a karkashin jagorancin Aminu Tambuwal suka je har gida suna zawarcin Segun Mimiko a lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugabanni.

Sauran gwamnonin su ne Seyi Makinde na Oyo, gwamnan Ribas Nyesom Wike da na Abia, Okezie Ikpeazu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel