An kashe abokin Gwamna Mimiko

An kashe abokin Gwamna Mimiko

An kashe tsohon shugaban rikon jam’iyar PDP na jihar Ondo Niyi Pirisola wanda kuma amini ne ga gwamnan jihar Ondo Mimiko.

 

An kashe abokin Gwamna Mimiko
Niyi Pirisola

Lamarin ya afku ne da safiyar ranar Juma’a 2 ga watan agusta, kamar yadda wani dan unguwar ya shaida ma Legit.ng, yace mamacin na kan hanyarsa ne ta dawo daga coci inda ya kwana yana ibada lokacin da aka sassare shi da adda a kofar gidansa dake Ilutitun Osoro.

Tuni an wuce da gawarsa babban asibitin karamar hukumar Okitipupa. An haife Niyi a ranar 3 ga watan janairu 1959.

Wani sanannen mawaki a jihar Ondo ya koka da kisan Niyi, inda yace “yanzu yin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare, yau kuma abin ya koma kisan kai. Don haka dole ne mu dinga sa ido, naji zafin mutuwar Niyi Pirisola”

Asali: Legit.ng

Online view pixel