Bayan Tafiyar Jami'an Amurka, 'Yan Ta'adda Sun Tsara kai Babban Hari Abuja, Neja

Bayan Tafiyar Jami'an Amurka, 'Yan Ta'adda Sun Tsara kai Babban Hari Abuja, Neja

  • Wani rahoto ya nuna cewa ana zargin 'yan ta'adda sun shirya kai hare-hare wasu muhimman wurare a birnin tarayya Abuja da jihar Neja
  • An bayyana cewa jami'an tsaro suna cikin shiri domin dakile duk wata barazana da harin da 'yan ta'addan zai iya haifarwa a wuraren
  • Rahoton zargin kai harin ya fito ne kwanaki kadan bayan Gwamnatin Amurka ta umarci jami'anta su rufe ofis su koma gida daga Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumomin tsaron Najeriya sun shiga cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon wata barazanar kai hari da 'yan ta'adda ke shirin yi kan muhimman gine-ginen gwamnati a Abuja da Neja.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da fuskantar barazanar tsaro a yankunan Najeriya a kwanan nan, musamman Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Amurka ta cafke wasu ƴan Najeriya 8 da ke ɗaukar nauyin ta'addanci? Gaskiya ta fito

Kofar shiga birnin tarayya Abuja
Kofar shiga Abuja a hagu, wasu 'yan bindiga a dama. Hoto: Zagazola Makama|Getty Images
Source: Facebook

Kamfanin dillancin labarai na AP ya sanar da cewa ya samu rahoton ne daga wata takardar sirri mai ɗauke da kwanan wata 13 ga Afrilun 2026 daga hukumar kwastam ta Najeriya.

Wuraren da ake zargi za a kai hari

Rahoton ya nuna cewa wuraren da aka tsara kai harin sun haɗa da filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da kuma gidan yari a birnin Abuja, da kuma wata cibiyar tsare sojoji a jihar Neja.

“Manufarsu ita ce su sako ‘yan ta’adda da ake tsare da kuma jawo babbar illa ga muhimman kayan aikin jiragen sama,”

In ji takardar.

Takardar ta nuna cewa wannan shiri ya yi kama da wani hari da aka kai kasar Nijar a watan Janairun 2026, inda ‘yan ta’adda suka kai hari kan sansanin sojojin sama a Niamey, a matsayin gargadi ga jami’an kwastam.

Takardar ta ce:

“Binciken rahoton ya nuna akwai dangantaka mai tayar da hankali tsakanin yiwuwar kai hari kan Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma hare-haren baya-bayan nan da aka kai kan filayen jiragen sama a Jamhuriyar Nijar,

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun bi 'yan ta'adda cikin daji sun musu barin wuta

"Musamman a Niamey da Tahoua. Wannan na nuna yiwuwar ‘yan ta’adda na ƙoƙarin maimaita irin wadannan hare-hare a Najeriya,”

Jami'an tsaro sun yi shiri a Abuja

Wani babban jami’in kwastam da bai da izinin magana da manema labarai ya shaida wa AP cewa hukumomi na cikin shiri domin dakile barazanar:

“Sojoji da sauran hukumomin tsaro suna cikin shirin ko-ta-kwana kuma a shirye suke su dakile harin.”

Rahoton TRT ya nuna cewa Hukumar Kwastam da rundunar sojin Najeriya ba su mayar da martani ba kan buƙatar jin ta bakinsu.

Taswirar jihar Neja
Taswirar jihar Neja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Amurka ta janye jami'ai a Abuja

A wani labarin, kun ji cewa a makon da ya gabata, Amurka ta ba da umarnin ma’aikatanta da ba na gaggawa ba da iyalansu su fice daga daga ofishin jakadancinta da ke Abuja.

Ta ba su umarni ne sakamakon ƙaruwar hare-haren ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma laifuffukan tashin hankali a ƙasar, musamman a Arewa.

Sai dai Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin matakin kariya na yau da kullum bisa ƙa’idojin aiki ba saboda rugujewar tsaro ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng