Jigon ADC Ya 'Gano' Halin da APC ke ciki, Ya Fadi Hadin da zai Kai Tinubu Ƙasa a 2027
- Jagora a jam'iyyar hamayya ta ADC Dele Momodu ya bayyana cewa APC mai mulki na cikin rudani gabanin babban zaben 2027
- Ya bayyana cewa ADC tana da karfin da za ta kora Bola Tinubu daga ofis musamman idan aka yi hadin Atiku Abubakar da Peter Obi
- Ya ce haɗin gwiwar na iya ƙarfafa ADC a zaɓe mai zuwa, sannan ya zargi APC da matsin lamba da hana ‘yan adawa rawar gaban hantsi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fitaccen ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar adawa, Dele Momodu, ya bayyana goyon bayansa ga yiwuwar haɗa tikitin shugaban ƙasa tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi a karkashin ADC gabanin zaɓen 2027.
Ya bayyana yakinin cewa hada wadannan mutane biyu a kan tikitin takarar shugaban kasa da mataimakinsa zai taimaka wajen kayar da APC a cikin sauki.

Source: Facebook
Momodu ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Talata, 14 ga watan Afrilu, 2026.
Momodu ya magantu kan takarar Obi da Atiku
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Dele Momudu ya bayyana cewa haɗin Atiku da Obi zai haifar da 'da mai ido saboda sun taba aiki tare a zaɓen 2019, wanda ya sa suke da fahimtar juna.
Ya ce:
“Zan haɗa shi (Atiku) da Peter Obi saboda sun taba yin aiki tare a 2019, don haka sun riga sun san juna. Peter Obi ya zo na uku a zaɓen da ya gabata, don haka ba sai an wahala sosai wajen jawo hankalin mutanen da ke goyon bayansa ba.”
Momodu ya nuna cewa irin wannan haɗakar na iya taimaka wa jam’iyyar ADC wajen jawo hankalin masu zaɓe, musamman ganin yadda Obi ke da farin jini a tsakanin wasu matasa da masu sauyi.
Momodu ya soki jam'iyyar APC
A yayin hirar, Momodu ya kuma soki jam’iyyar APC mai mulki, inda ya zargi jam’iyyar da fuskantar matsin lamba duk da ƙoƙarin Bola Ahmed Tinubu na tattara goyon bayan gwamnoni, ministoci da ‘yan majalisa.
Ya ce:
“Ba su yarda cewa za a iya samun manyan shugabannin adawa guda huɗu ko biyar a ƙasar nan ba. Wasu kuma suna ƙoƙarin raunana su domin kada su zama barazana.”

Source: Facebook
A cewarsa:
“Gaskiya ce, kada mu ɓoye. Duk da cewa Tinubu ya tattara gwamnoni da sauran manyan mutane, ana ganin yadda 'yan jam'iyyar suka tsorata."
Momodu ya kuma zargi APC da hana mambobinta faɗin ra’ayinsu, yana mai cewa da dama daga cikin abokansa a jam’iyyar suna jin tsoro su bayyana abin da ke ransu.
Jigon ADC ya dura kan Tinubu
A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da takura wa jam’iyyun adawa a kasar nan.
Ya bayyana zargin cewa gwamnatin ta nemi a hana su dakin taron jam'iyyar hamayya ta ADC, yana nuna cewa ana kokarin shake jam'iyyar hamayya ta kasa domin hana su katabus.
Mista Peter Obi, ya gargadin cewa tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya na fuskantar barazana yayin da ake shirin babban zaɓen 2027 da zai dauki hankalin duniya, musamman ganin shirin 'yan siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


