"Na Ji Kunya": Tinubu Ya ba EFCC Umarnin Bude Asusun Gwamnatin Osun da Aka Rufe
- Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumar EFCC ta koma kotu domin janye umarnin daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun
- Tinubu ya ce lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba saboda zaɓen gwamnan Osun ya rage saura kwanaki kaɗan
- Shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta 'yancin hukumomin bincike su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma baki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Abuja – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ta gaggauta komawa kotu domin janye umarnin da ya ba ta damar rufe asusun gwamnatin jihar Osun.
Tinubu ya bayyana cewa ya damu da lokacin da aka ɗauki wannan mataki kasancewar jihar Osun na dab da gudanar da zaɓen gwamna.

Kara karanta wannan
Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Source: Twitter
Abin da Tinubu ya ce kan EFCC
Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya fitar da kalaman Tinubu a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 6 ga Agusta, 2026.
Ya ce duk wani mataki da wata hukuma ta gwamnatin tarayya ta ɗauka, jama'a kan ɗora alhakin hakan a kansa a matsayinsa na shugaban ƙasa, ko da kuwa bai san da lamarin ba tun farko.
"Hakika, dole in bayyana cewa na ji kunya sosai, ba wai da matakin da EFCC ta dauka bisa umarnin kotu ba, a a, sai dai saboda lokacin da hukumar ta dauki wannan mataki."
- Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa tun bayan hawansa mulki ya bai wa EFCC da sauran hukumomin bincike cikakken 'yanci su gudanar da ayyukansu cikin 'yanci, ba tare da tsoma bakin gwamnati ko son rai ba.
"Bai kamata jama'a su yi zargi ba"
Sai dai ya ce duk da cewa har yanzu ba a yi masa cikakken bayani kan dalilan da suka sa EFCC ta nemi umarnin kotun ba, ya yi imanin cewa lokacin da aka ɗauki matakin bai dace ba.
Tinubu ya ce bai kamata a yi wani abu da zai sa jama'a su yi zargin cewa ana amfani da wata hukuma ta gwamnatin tarayya wajen yin tasiri a harkokin zaɓe ba, musamman yayin da zaɓen gwamnan Osun ya rage saura kwanaki kaɗan.
A cewarsa:
"Nan da 'yan kwanaki ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar Osun. A don haka, bai kamata a aikata wani abu da zai cusa wa mutane zargin cewa ana amfani da EFCC ko duk wata hukumar gwamnatin tarayya don tsoma baki a harkokin zaben ba."
Umarnin da shugaban ƙasa ya bayar
Tinubu ya bayyana cewa saboda kare mutuncin tsarin dimokuraɗiyya da tabbatar da amincewar jama'a ga hukumomin gwamnati, ya zama wajibi ya shiga tsakani.
Ya ce saboda haka ne ya umarci EFCC da ta gaggauta komawa kotu domin ta nemi a soke umarnin daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun tare da janye duk wani matakin shari'a da ta fara kan lamarin.
Shugaban ƙasar ya kuma sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta 'yancin hukumomin gwamnati su gudanar da ayyukansu bisa doka, amma ya ce ya zama dole a yi la'akari da lokacin ɗaukar wasu matakai domin kauce wa haifar da shakku a tsakanin jama'a.
Sanarwar ta biyo bayan umarnin kotun da EFCC ta samu a ranar 5 ga watan Agustan 2026 na daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce gabanin zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng

