Zargin ta'asa: Koto ta soke zarge-zarge 19 a cikin 21 da ake yi wa Sanata Goje

Zargin ta'asa: Koto ta soke zarge-zarge 19 a cikin 21 da ake yi wa Sanata Goje

Wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Jos, jihar Filato a ranar Juma'a ta soke zarge-zarge 19 a cikin 21 da ke gaban ta na tuhuumar zargin ta'asar da ake yi wa tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje da wasu mutane uku.

Su dai mutanen dukkan su hudun a baya an shigar da karar su ne a gaban kotun ana zargin su da laifin karkatar da sama da Naira biliyan shida na dukiyar al'umma a jihar ta Gombe lokacin mulkin Gwamnan.

Zargin ta'asa: Koto ta soke zarge-zarge 19 a cikin 21 da ake yi wa Sanata Goje
Zargin ta'asa: Koto ta soke zarge-zarge 19 a cikin 21 da ake yi wa Sanata Goje
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An gargadi Buhari kan karin haraji

Hukumar nan dake yaki da masu cin hanci da rashawa ta Economic and Financial Crimes Commission, EFCC ce dai a maimakon gwamnatin tarayya ta shigar da karar gaban kotun tun a shekarar 2011 kuma har yanzu ake ta cakusawa.

Sauran wadanda ake tuhumar tare da Sanata Goje da yanzu ke wakiltar mazabar jihar Gombe ta tsakiya sun hada da tsohon shugaban hukumar ilimi ta bai-daya a jihar watau state Universal Basic Education Board (SUBEB), Alhaji Aliyu Ubandoma El-Nafaty.

Sauran kuwa sun hada da wani mai samar wa da jihar abinci watau Sabo Tumu tare da wani babban dan kwangila da yanzu haka Allah yayi masa cikawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel