Shararren Mawakin Siyasar Abba Gida Gida Ya Rasu, An Yi Babban Rashi a Kano
- Fitaccen mawakin siyasa Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, ya rasu a wani asibiti da ke Kano ranar Lahadi
- Kosan Waka ya shahara da waƙoƙin siyasa, musamman waƙar "Abba ka cika gwarzo" da ya yi wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
- Kafin rasuwarsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai masa ziyara a asibiti domin duba lafiyarsa, lamarin da ya jawo hankalin jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kano - An shiga jimami bayan rasuwar fitaccen mawakin siyasa na Kano, Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da Kosan Waka, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 2 ga Agustan 2026, a wani asibiti da ke jihar Kano.
Rasuwar mawakin ta jefa iyalansa, 'yan'uwansa, abokansa, masoya da sauran al'umma cikin alhini, musamman waɗanda suka san shi da kuma waɗanda suka kasance suna bibiyar ayyukansa a fagen waƙa.

Source: Facebook
Kosan Waka ya yi fice a waƙoƙin siyasa
Fitaccen mawakin siyasa, Tijjani Gandu ne ya sanar da rasuwar a shafinsa na Facebook, haka zalika, shi ma mawaki Abubakar Sani ya sanar da rasuwar a shafinsa na Facebook.
Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun mawakan siyasa a Arewacin Najeriya, inda waƙoƙinsa suka samu karɓuwa sosai a tsakanin masoya.
Ya shahara musamman da waƙar "Abba ka cika gwarzo", wadda ya rera domin yabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Salon waƙarsa na musamman da kuma saƙonnin da ke cikin waƙoƙinsa sun sa ya zama sananne a harkokin siyasar jihar Kano.
Gwamna Abba ya ziyarce shi kafin rasuwarsa
A ƙarshen watan Yuli, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai wa Kosan Waka ziyara a asibitin da yake kwance domin duba lafiyarsa.
Bidiyon ziyarar ya Labari da Gaskiya ya wallafa a Facebook, ya nuna gwamnan yana nuna damuwa kan halin da mawakin yake ciki, tare da tattaunawa da likitan da ke kula da lafiyarsa.
Mutane da dama sun bayyana ziyarar a matsayin alamar girmamawa ga gudunmawar da marigayin ya bayar a fagen waƙoƙin siyasa.
Masoya sun yi jimamin rasuwarsa
Rahotannin farko sun nuna cewa labarin rasuwar Kosan Waka ya bazu cikin gaggawa a tsakanin masoyansa da abokan sana'arsa, lamarin da ya jefa mutane da dama cikin jimami.
Masu bibiyar harkokin Kannywood da siyasa sun fara aikewa da saƙonnin ta'aziyya tare da addu'ar Allah Ya jikansa da rahama.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan musabbabin rasuwarsa ko kuma lokacin da za a gudanar da jana'izarsa ba.
Iyalan marigayin da masoyansa na ci gaba da karɓar gaisuwar ta'aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan, yayin da ake ci gaba da yi masa addu'ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa, Ya haskaka kabarinsa, Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsa, tare da bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Asali: Legit.ng

