Nasir El Rufai Ya Samu Beli bayan Dogon Lokaci ana Shari'a a Kotu

Nasir El Rufai Ya Samu Beli bayan Dogon Lokaci ana Shari'a a Kotu

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya halarci zaman kotu a ranar Talata, 14 ga watan Afirilun 2026.
  • A yayin zaman kotun, tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya samu beli wanda zai sanya ya bar hannun hukumomin tsaron da ke ci gaba da tsare shi
  • Dan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai, wanda yake dan majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa suna kokarin ganin sun cika sharuddan belin da aka ba mahaifinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya samu beli a a gaban kotu.

Hon. Bello El-Rufai, ɗan tsohon Gwamna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kaduna ta bayar da belin mahaifinsa.

El-Rufai ya samu beli a kotu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton samun belin na Nasir El-Rufai a ranar Talata, 14 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Dalilin kotun Kaduna na sake 'dage shari'ar neman belin Nasir El Rufa'i

Kotu ta ba da belin Nasir El-Rufai

A cewar ɗan majalisar tarayyar, wanda ya kasance a cikin zauren kotun inda aka hana manema labarai shiga, ya ce a halin yanzu iyalinsa suna kan ƙoƙarin cika sharuɗɗan belin.

“Muna farin ciki da aka ba Malam beli. Za mu cika sharuɗɗan belin domin mun yi amanna da bin doka da oda."

- Bello El-Rufai

Ƙoƙarin jin ta bakin lauyan wanda ake ƙara, Ubong Akpan (SAN), bai yi nasara ba domin ya ƙi cewa uffan, inda ya bayyana cewa babban lauyan tawagar ne zai yi magana da manema labarai.

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa mai shari'a, Rilwan Aikawa, ne ya amince da bukatar belin El-Rufai.

An gindaya masa sharudda

Haka zalika, wani jigo a jam’iyyar ADC kuma na kusa da El-Rufai, Hayatudeen Lawal Makarfi, ya tabbatar da batun, inda ya ce akwai wasu sharuɗɗa da aka gindaya wa belin.

Malam Nasir El-Rufai ya samu beli
El-Rufai yayin da yake shiga harabar kotu Hoto: @ADCVanguard
Source: Facebook

Ya nuna kyakkyawan fatan cewa za su cika waɗannan sharuɗɗan nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta sanya lokacin yanke hukunci kan bukatar belin El Rufai

Idan za a iya tunawa, tun da fari Hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai ne a gaban babbar kotun jihar Kaduna, inda aka ɗage saurarar buƙatar belin tasa zuwa ranar 21 ga Afrilu, 2026.

Sai dai wannan sabon hukuncin ya fito ne daga wata babbar kotun tarayya ta daban.

Karanta karin wasu labaran kan El-Rufai

Jami'an tsaro sun cafke Nasir El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na hukumar farin kaya (DSS), sun cafke tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon Ministan birnin tarayya Abuja, Nasir Ahmad El-Rufai.

Jami'an hukumar DSS sun cafke tsohon gwamnan na jihar Kaduna ne a harabar babbar kotun tarayya da ke Kaduna.

Hakazalika, jami’an DSS sun tafi da tsohon gwamnan ne bayan da kotun ta ɗage lokacin yanke hukunci kan buƙatar tasa ta neman beli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng