G Fresh Ya Saki Bidiyo kan Mutuwar Auren Adam A. Zango da Jarumar Kannywood

G Fresh Ya Saki Bidiyo kan Mutuwar Auren Adam A. Zango da Jarumar Kannywood

  • Shahararren dan TikTok, G-Fresh Al-Amin ya soki jarumin Kannywood, Adam Zango kan abin da ya jawo rabuwarsa da matarsa
  • Tun farko Jarumi Adam Zango ya ce sun rabu da Maimuna Pretty cikin lumana domin kauce wa haihuwar yara masu cutar sikila
  • Jarumin Kannywood ya taba yin aure sau shida, kuma dukkansu sun kare da saki, lamarin da ya sa ake yawan magana a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Fitaccen tauraron TikTok da ke Kano, G-Fresh Al-Amin, ya caccaki jarumin Kannywood Adam, Zango bayan rabuwarsa da matarsa ta shida, Maimuna Pretty.

G-Fresh ya bayyana cewa dalilin da jarumin ya bayar na rashin dacewar kwayoyin halitta (genotype) ba shi da ma'ana kuma bai kamata a bayyana shi a kafafen sada zumunta ba.

G Fresh.
Shaharraren dan TikTok a Arewacin Najeriya, G-Fresh Al-Amin Hoto: G-Fresh Al-Amin
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wani bidiyo da ya wallafa a TikTok tare da wata mata da ake kyautata zaton ita ce matarsa, wadda ta yi magana daga bayan kyamara ba tare da ta fito fili ba.

Kara karanta wannan

"Har yanzu harsashi na jikina bayan zanga zangar yunwa": Matashin Kano

Shahararren dan Tik-Tok din, wanda shi ma yana yawan rabuwa da matansa, ya ce maganar da Adam Zango ya yi ta janyo masa abin dariya ne kawai.

Adam Zango ya saki jarumar Kannywood

A kwanakin baya, Adam Zango ya tabbatar da rabuwarsa da Maimuna Musa, wacce aka fi sani da Maimuna Pretty.

Jarumin ya bayyana cewa sun yanke shawarar rabuwa ne bayan sun gano cewa dukkansu sun kasance AS, domin kauce wa yiwuwar haihuwar yara masu fama da cutar sikila.

Har ila yau, ya wallafa bidiyon tsohuwar matarsa tana barin gidansa, yana mai tabbatar da cewa sun rabu cikin fahimtar juna tare da gargadin jama'a kada su yada jita-jita game da lamarin.

G-Fresh ya soki Adam A. Zango

G-Fresh Al-Amin da matarsa sun ce gwajin genotype yana daga cikin muhimman gwaje-gwajen da ake yi kafin aure, saboda haka ba su fahimci yadda za a kai ga aure ba tare da sanin sakamakon ba.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sanya na saki matata Maimuna Pretty, Adam A Zango ya yi bayani

Ya ce:

"Ba zai yiwu mutum ya yi gwajin HIV kadai ba tare da yin cikakken binciken lafiya da ya hada da gwajin genotype kafin aure ba."
Zango.
Jarumin Kannywood, Adam A. Zango da tsohuwar matarsa, Maimuna Musa Hoto: Adam A. Zango
Source: Facebook

Sun kuma bayyana cewa bai dace Adam Zango ya wallafa wannan bayani a kafafen sada zumunta ba, domin hakan ba ya ilmantar da jama'a, sai dai ya bude kofar suka da izgili.

A cewarsu:

"Ba ka bin kowa bashin bayani. Da ka yi shiru kawai ya fi."

G-Fresh ya kara da cewa ko da zai shiga wata sabuwar alaka da wata mace, dole ne ta fara yin cikakken gwajin lafiya kafin a ci gaba da maganar aure.

Abin da ya kashe auren Adam A. Zango

A baya, kun ji cewa Jarumi Adam A. Zango ya tabbatar da rabuwarsa da matarsa, Maimuna Musa, inda ya bayyana cewa dukkansu suna da genotype iri daya.

Jarumin ya ce ya ga ya dace ya bayyana wannan bayani domin jama'a su san gaskiyar abin da ya faru, maimakon ci gaba da yaɗa jita-jita ko bayanan da ba su da tushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262