Wata Sabuwa: El Rufai Ya Burma cikin Matsala bayan Zaman Kotu

Wata Sabuwa: El Rufai Ya Burma cikin Matsala bayan Zaman Kotu

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kawo Malam Nasir Ahmad El-Rufai gaban kotu yayin da ake ci gaba da shari'a
  • Kotun ta dage lokacin da za ta zartar da hukunci kan bukatar da tsohon gwamnan ya nema ta a bayar da belinsa
  • Jim kadan bayan tashi daga zaman kotun, jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun yi caraf da tsohon gwamnan na Kaduna

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Jami'an hukumar DSS sun cafke tsohon gwamnan na jihar Kaduna ne a harabar babbar kotun tarayya da ke Kaduna.

Jami'an DSS sun cafke El-Rufai
Malam Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa jami'an na DSS sun cafke El-Rufai ne a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Kotu ta sake dage shari'ar El-Rufa'i, zai san makomarsa nan da makonni 2

Hukumar DSS ta cafke Nasir El-Rufai

Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da sauran laifuffuka masu alaƙa (ICPC) ne suka kawo El-Rufai kotun a ranar Laraba domin saurarar buƙatarsa ta neman beli.

Sai dai, jami’an DSS sun tafi da tsohon gwamnan ne bayan da kotun ta ɗage lokacin yanke hukunci kan buƙatar tasa ta neman beli zuwa ranar 14 ga Afrilu.

A ranar 24 ga Maris, hukumar ICPC ta gurfanar da El-Rufai da Joel Adoga kan zarge-zargen da suka shafi damfara da halatta kuɗaɗen haram. Waɗanda ake ƙara sun musanta zarge-zargen.

El-Rufai na da kwarin gwiwa kan beli

Yayin da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, Oluwole Iyamu, jagoran lauyoyin tsohon gwamnan, ya ce suna da kyakkyawan fata kan hukuncin da kotun za ta yanke game da neman belin.

“An tattauna kan buƙatar neman belin kuma an ba da martani, sannan an tsayar da ranar 14 ga Afrilu domin yanke hukunci. Muna jiran wannan rana kuma muna da kyakkyawan fata."

Kara karanta wannan

El Rufai zai ci gaba da zama hannun ICPC duk da rasuwar mahaifiyarsa

“Mun gabatar da hujjojinmu a gaban kotu, kuma wannan kotu ce ta adalci. Muna jiran matsayar kotun.”

- Oluwole Iyamu

DSS ta yi caraf da El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

DSS za ta fafata da El-Rufai a kotu

Game da shari’ar da DSS ta shigar kan El-Rufai wadda aka shirya yi a ranar 10 ga Afrilu a babbar kotun tarayya da ke Abuja, Iyamu ya ce an riga an shigar da dukkan takardun da suka dace, rahoton The Punch ya tabbatar da hakan.

“Wannan magana ce ta daban. A matsayinmu na lauyoyi, muna nan a shirye. Mun shigar da dukkan takardun da suka dace kuma za mu kasance a kotu. Wannan ita ce maganar DSS."

- Oluwole Iyamu

A watan Fabrairu, hukumar DSS ta shigar da ƙara mai ƙunshe da tuhume-tuhume guda uku kan El-Rufai dangane da zargin saurare da naɗar hirar waya ba bisa ƙa’ida ba, biyo bayan kalaman da ya yi a wata hira da gidan talabijin.

El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun ICPC

A wani labarin kuma, kun ji cewa an mayar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai hannun hukumar ICPC.

Kara karanta wannan

Matakin da alkali ya dauka kan bukatar beli a shari'ar El Rufai da hukumar ICPC

Nasir El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun hukumar ICPC bayan ta sake shi na wasu 'yan kwanako domin ya yi jana'izar mahaifiyarsa.

Bayan bayyanar El-Rufai a kotu, an mayar da shi hannun hukumar ICPC yayin da ake ci gaba da gudanar da shari’o’in da ake yi kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng