'Barci ba Naka Ba ne,' Malamin Addini Ya Zaburar da Tinubu kan Haɗakar ADC
- Babban Fasto a Najeriya, Primate Elijah Ayodeleya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya kasance cikin shiri
- Yana ganin ADC na iya zama barazana ga APC a zaɓen 2027, tare da cewa jam’iyyar na fuskantar rikici daga cikin gida
- Ya shawarci yan adawa da su kara hada kai a ADC, domin akwai alamun cewa sun biyo hanyar da za ta kai su ga ci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya aika da gargaɗi mai zafi ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya sanar da shi cewa ya kamata ya kasance cikin shiri da hankali kan jam’iyyar ADC, wacce ke samun karbuwa a matsayin dandalin haɗin gwiwar ’yan adawa.

Asali: Facebook
Nigerian Tribune ta wallafa cewa, malamin ya bayyana jam’iyyar APC ta fara yin wasu kura-kurai da ka iya janyo mata faduwa a babban zaɓen 2027 mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Elijah Ayodele ya gargadi Bola Tinubu
Primate Ayodele ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da Ubangijinsa ya nuna masa dangane da babban zaɓen shekarar 2027.
Ya kara da cewa akwai cikakken bayani kan abubuwan a cikin littafinsa mai suna "Warnings to the Nations", wanda za a kaddamar a ranar 5 ga Yuli, 2025.
Littafin, wanda ke fitowa duk shekara tun daga 1994, na ɗauke da hasashensa game da shugabanni, ƙasashe da manyan attajirai a duniya.
A wannan karon, ya nuna cewa za a samu hasashen game da zaɓen shugaban a 2027, shugaban Ghana John Mahama, da manyan ’yan kasuwa irinsu Mike Adenuga, Aliko Dangote, da Abdul Samad Rabiu.
Ayodele ya yi na'am da ADC
A wani ɓangare na jawabinsa, Primate Ayodele ya shawarci ’yan adawa da su guji amfani da jam’iyyar ADA a matsayin dandalin haɗin gwiwa domin babu haske.

Asali: Twitter
Ya ce:
“Jam’iyyar ADA ba za ta ba ku komai ba. ADC ta fi dacewa da irin wannan haɗaka. Har ma SDP ba za ta iya motsa komai ba. Su yi amfani da ADC don kada su gina gini a kasa mara albarka."
Primate Ayodele ya ce jam’iyyar na da cikakkiyar damar gina sabuwar hanyar siyasa da za ta dace da bukatun talakawa, yayin da rikici ke shirin kunnowa APC.
A kalamansa:
“Taron gangamin jam’iyyar APC zai zama matakin farko na rikicin cikin gida da zai kunno kai. Tinubu bai kamata ya yi sakaci ba, domin matsaloli na zuwa, kuma har yanzu ba su fahimta ba."
Ayodele ya yi hasashe kan magajin Tinubu
A baya, mun wallafa cewa shugaban cocin INRI Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan magajin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
Ya ce mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, shi ne zai zama shugaban Najeriya bayan kammala wa’adin Tinubu.
Primate Ayodele ya bayyana cewa Tinubu zai yi wa’adin mulki na biyu, kuma bayan kammala shi a 2031, Nuhu Ribadu ne zai zama shugaban ƙasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng