"Muna PDP, Muna Hadakarsu Atiku," Sule Lamido Ya ce za Su Yi Koyi da Wike

"Muna PDP, Muna Hadakarsu Atiku," Sule Lamido Ya ce za Su Yi Koyi da Wike

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana takaici a kan yadda Nyesom Wike ke kokarin mayar da PDP cikin aljihunsa
  • Sule ya bayyana cewa yana maraba da kowace haɗin gwiwa da za ta taimaka wajen kalubalantar gwamnatin Bola Tinubu a 2027
  • Ya yi zargin cewa yanzu haka, PDP ta koma kamar mallakinshugaban kasa Bola Tinubu saboda ayyukan Wike da Mutanensa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido, ya bayyana cewa yana maraba da duk wata haɗin gwiwa da za a yi domin fuskantar gwamnatin Bola Tinubu a 2027.

Tsohon gwamnan ya yi wannan karin haske ne bayan an hango hotonsa tare da wasu daga cikin jiga-jigan ’yan siyasa da suka amince da haɗakar da ADC don tumbuke APC daga mulkin Najeriya.

Atiku Abubakar da Sule Lamido
Sule Lamido ya ce yana tare da ADC Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A wata hira da Sule Lamido ya yi da DCL Hausa da aka wallafa a shafin Facebook, ya ce yana goyon bayan ADC domin a kai ga nasarar kafa sabuwar gwamnati bayan babban zaɓen 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC: Sule Lamido ya magantu kan barin PDP

Jigo a PDP kuma tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana takaicin yadda jam'iyyarsa zuba idanu a kan wasu tsirarun ’yan jam’iyya suna aikata abin da suka ga dama.

Ya ce:

“Babu yadda za a ce a yi jam’iyya tana hamayya, amma a ce shugabanninta da wasu manyan ’ya’yanta su ce sun yanke hukuncin cewa za su zabi jam’iyya mai mulki.”

Sule Lamido ya ce wannan ya nuna cewa babu kishin jam’iyya ko kokarin mutunta dokokin da suka samar da PDP a matsayinta na jam’iyya mai zaman kanta.

Ya kuma ce abin da ya yi bai yi kama da cin dunduniyar jam’iyyar PDP ba, illa dai ya yi hakan ne domin a haɗu da sauran ’yan Najeriya masu kishin kasa.

Sule Lamido ya fusata

Sule Lamido ya bayyana matuƙar takaici a kan yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike da yaransa ke kokarin mayar da PDP tamkar mallakar su.

Ya ce Wike da ’yan barandansa na kokarin tilasta wa kowa goyon bayan Bola Tinubu, inda ya ce sam ba za su bari wasu tsirarun mutane su yi nasara ba.

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Sule Lamido ya zargi Nyesom Wike da mayar da PDP aljihunsa Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

Sule Lamido ya ce kamar yadda Wike da ’yan barandansa ba za su iya korarsa da sauran waɗanda suka wahala wajen gina PDP daga cikin jam’iyyar ba.

Ya ce:

“Ni ina PDP, duk abin da ake yi a cikin PDP, kodayake yanzu PDP ta rabu gida biyu, akwai masu bangaren Tinubu, to ni zan je bangaren mutanen da ke da kishin kasa domin mu haɗa kai a cikin haɗaka.”

Sule Lamido ya gana da Atiku Abubakar

A baya, mun wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yana ganawar sirri da wasu manyan jam’iyyar PDP a ranar Talata, 1 ga Yuli, 2025 a Abuja.

Wannan ganawa ta musamman na gudana ne a wani ɓangare na shirin haɗin gwiwar siyasa da ake cigaba da tattaunawa a kai, domin fuskantar 2027.

Daga cikin waɗanda suka halarci wannan ganawa akwai tsohon shugaban majalisar dattawa, da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.