'Zuwansa Alheri ne': Ribadu Ya Faɗi Yadda Tinubu Ya Ceto Najeriya daga Tarwatsewa

'Zuwansa Alheri ne': Ribadu Ya Faɗi Yadda Tinubu Ya Ceto Najeriya daga Tarwatsewa

  • Nuhu Ribadu ya ce Najeriya na dab da rugujewa a 2022 saboda matsalolin tsaro, amma Bola Tinubu ya ceto kasar tun 2023
  • Ribadu ya bayyana cewa an kashe 'yan ta’adda fiye da 13,500, sannan sama da 124,000 daga Boko Haram da ISWAP da iyalansu sun mika wuya
  • Ya ce gwamnati na bukatar taimakon tsofaffin sojoji, yayin da Azubuike Ihejirika ya bukaci dukan matasan NYSC su samu horaswar soja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana irin gudunmawar da gwamnatin Bola Tinubu ta bayar.

Ribadu ya ce Najeriya ta kai wani mummunan matsayi a 2022, tana fuskantar rikice-rikicen da suka barazana ga haɗin kan ƙasa.

Ribadu ya yabawa abin alheri da Tinubu ya kawo Najeriya
Ribadu ya ce Tinubu daga wargajewa. Hoto: Nuhu Ribadu, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Nuhu Ribadu ya fadi halin da Najeriya ta shiga

Ribadu ya fadi haka ne yayin da yake jawabi a Abuja, a bikin cika shekaru 50 na kammala karatu na rukuni na 18 a makarantar NDA, cewar Channes TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban EFCC ya ce Najeriya ta shiga matsala daga zaman lafiya, da makomarta, kafin shugaban ƙasa Bola Tinubu ya hau mulki a 2023.

Ya bayyana halin da ake ciki a wancan lokacin a matsayin mai muni, yana mai cewa barazanar tsaro ta shafi kowane yanki na ƙasar.

Ya ce ƙalubalen sun mamaye sassa daban-daban, daga Arewa maso Gabas da ta fama da Boko Haram, zuwa Arewa maso Yamma mai cike da rikice-rikice.

Ribadu ya fadi adadin miyagu da aka hallaka

Hadimin ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin Tinubu na shawo kan abin da ya kira “ƙalubalen tsaro da aka gada, masu wahala da sarkakiya.”

A cewarsa, an ɗauki “matakai masu tsauri” domin dawo da zaman lafiya da kuma gina sabuwar kwarin gwiwar ƙasa baki ɗaya.

Ya bayyana cewa kokarin da ake yi wajen yaki da ta’addanci ya kai ga hallaka fiye da 'yan ta’adda da masu laifi 13,500, yayin da fiye da 124,000 daga Boko Haram da ISWAP da iyalansu suka mika wuya.

Ribadu ya fadi yadda Tinubu ya ceto Najeriya
Nuhu Ribadu ya yabawa Bola Tinubu a Najeriya. Hoto: Nuhu Ribadu.
Asali: Twitter

Ribadu ya ba da shawara kan matsalolin tsaro

Ribadu ya kuma ba da shawarar amfani da tsofaffin sojoji a yaƙi da rashin tsaro, yana mai jaddada mahimmancin ƙwarewar su wajen fuskantar barazana mai sarkakiya.

Haka kuma, tsohon hafsan sojin ƙasa na 22, Laftanar Janar Azubuike Ihejirika, ya bukaci a rika ba da cikakkiyar horaswar soja ga dukkan ‘yan hidimar NYSC.

Ya bayyana wannan a matsayin wata dabarar da za ta ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro a faɗin ƙasa.

APC ta nesanta Ribadu da harin kujerar Shettima

Kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa ta fito ta nesanta kanta daga batun marawa Nuhu Ribadu baya don neman wani muƙamin siyasa.

Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a cikin rahotannin da aka yaɗa masu nuna hakan.

Kalaman APC na zuwa bayan an fara hasashen wasu jiga-jiganta daga Adamawa na son a maye gurbin Kashin Shettima da Ribadu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.