Diyar tsohon shugaban majalisa, David Mark ta koma APC
- Diyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark da mogaya bayanta sun fice daga jam'iyyar APGA ta koma APC
- Blessing Mark, sanata mai wakiltar Otukpo/Ohimini ta shawarci sauran 'yan APGA da PDP a mazabar Benue ta Kudu su shigo APC
- A cewar Blessing, jam'iyyar PDP ta mutu har an birne ta don haka kowa ya shigo APC don ita zata karbe mulki a jihar
Blessing Onu Mark, diyar tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, a karshen mako ta yi wa daruruwan mambobi da magoya bayan jam'iyyun APGA da PDP jagora zuwa jam'iyyar APC a jihar Benue.
Blessing, yar majalisar tarayya ce da ke wakiltar mazabar Otukpo/Ohimini na jihar Benue.
The Nation ta ruwaito cewa mambobin wasu jam'iyyun siyasa a jihar suma sun sauya sheka zuwa jam'iyyar ta APC.
DUBA WANNAN: Hotuna: Ganduje ya tafi ta'aziyya Danbatta, ya bada N1.6m ga iyalan mutum 16 da suka rasu
Ta lashe zaben kujerar wakilcin Otukpo/Ohimini a karkashin inuwar jam'iyyar APGA, inda ta kayar da 'yan takarar PDP da APC a 2019.
A ranar Asabar, ta sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da magoya bayan ta a mazabar Benue ta Kudu tare da kananan hukumomi tara.
Da ta ke jawabi yayin taro a Otukpo hedkwatan mazabar Benue ta Kudu, Blessing ta bayyana cewa PDP ta mutu an kume birne ta a Zone C don haka ta bukaci sauran yan PDP su koma APC.
KU KARANTA: Masoyin Buhari ya ce shugaban kasar ya yi murabus bayan sace yan uwansa a Katsina
Ta ce APC ce za ta karbe mulki a Jihar Benue, "don itace jam'iyyar da kowa ya dace ya shiga."
Daruruwan mutane daga wasu jam'iyyun sun shiga APC sannan an basu katin kasancewa dan jam'iyya.
A wani labarin daban, mashahurin attajirin Brazil dan asalin kasar Lebanon Joseph Safra, ya rasu ranar Alhamis ya na da shekara 82, a cewar bankinsa.
Safra, wanda kiyasin dukiyar ya kai kimanin $23.2 biliyan, wanda ya zo na 63 cikin jerin masu kudin duniya da mujallar Forbes ta fitar.
An haife shi a 1938 ga wasu iyalai Yahudawa a Beirut, yayi hijira shi da Iyalan sa zuwa Brazil, inda mahaifin sa ya samar da inda ake kira Banco Safra.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng