Harin Ramuwar Gayyar Iran Ya Jikkata Jami'an Amurka a Kuwait

Harin Ramuwar Gayyar Iran Ya Jikkata Jami'an Amurka a Kuwait

  • Wasu sojojin Amurka da ma’aikatan kwangila sun samu raunuka bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait
  • Rundunar tsaron CENTCOM ta bayyana cewa jami’an tsaron Kuwait sun yi nasarar tare makamin kafin ya kai ga inda aka nufa ko yin wata babbar illa
  • Iran ta ce ta kai harin ne a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ta kai a wasu yankunan Kudancin ƙasar duk da magana da ake yi don yin sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Sojojin Amurka huɗu tare da wasu ma’aikatan kwangila uku sun samu raunuka sakamakon harin makami mai linzami da Iran ta kai kan wani sansanin soji da ke ƙasar Kuwait a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargin sun sace dalibai 300 a Papiri

An rawaito cewa dukkannin mutanen bakwai da suka samu raunukan sun koma bakin aikinsu cikin sa’o’i 24 bayan faruwar lamarin, kamar yadda wani jami’in Amurka ya tabbatar.

Iran ta kai hari sansanin Amurka a Kuwait
Shugaban Amurka Donald Trump, jagoran addini na Iran Mojtaba Khamnei Hoto: Donald J Trump/Imam Sayyid Mojtaba Khamnei
Source: Getty Images

A ruwayar CBS, an samu tabbacin cewa harin bai yi wata gagarumar illa ba, domin dukkanin jami'an da ma'aikatan kananan raunuka kawai suka samu.

An dakile harin Iran

Bloomberg ta ruwaito cewa tun da farko, rundunar Amurka ta CENTCOM ta sanar da cewa Iran ta harba wani makami mai linzami zuwa ƙasar Kuwait da 10.17 na dare agogon Gabashin Amurka a ranar Laraba 27 ga watan Mayu, 2026.

Sai dai jami’an tsaron Kuwait sun yi nasarar dakile makamin tun kafin ya isa inda aka nufa, lamarin da ya taimaka wajen rage barnar da ka iya faruwa.

Duk da cewa an samu wasu ƙananan raunuka ga wasu daga cikin jami’an Amurka da ma’aikatan da ke aiki tare da rundunar, babu rahoton asarar rayuka ko wata babbar illa da harin ya haifar.

Iran ta ce martani ta mayar

A ranar Alhamis, 28 ga watan Mayu, 2027, rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta fitar da sanarwa inda ta ce ta kai hari kan wani sansanin sojin Amurka domin mayar da martani ga hare-haren da Amurka ta kai a Kudancin ƙasarta.

Kara karanta wannan

Sojoji da 'yan ta'adda sun gwabza kazamin fada a Kogi, an rasa rayuka

Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne
Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamnei Hoto: Imam Sayyid Mojtaba Khmanei
Source: Getty Images

Sai dai sanarwar ba ta fayyace takamaiman sansanin da aka kai wa harin ba a lokacin da ita kanta Amurka ke ikirarin ta kai harin 'kare kai' zuwa cikin kasar Iran.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali tsakanin Iran da Amurka, inda ɓangarorin biyu ke musayar zarge-zarge da matakan soja a yankin Gabas ta Tsakiya.

Har yanzu hukumomin Kuwait ba su fitar da cikakken bayani kan illar harin ba, yayin da jami’an Amurka ke ci gaba da bibiyar halin da ake ciki domin tabbatar da tsaron dakarunsu da cibiyoyinsu a yankin.

Iran ta harbo jirgin yakin Amurka

A baya, kun ji cewa ana cigaba da zaman doya da manja tsakanin gwamnatin Iran da Amurka karkshin shugaban kasa Donald Trump duk da tsagaita wutar yaki da aka cimma da taimakon Pakistan.

A ranar Alhamis, 28 ga watan Mayun 2026, dakarun Iran sun bayyana cewa sun harbo wani jirgin Amurka da ya shiga sararin samaniyarsu, wanda ake kyautata zaton yana barazana ga tsaron kasar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace tsohon manjo janar da matarsa a Katsina

Jim kadan bayan fitar da labarin, gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi martani, inda ta yi karin haske game da abin da kasar Iran ta fada yayin da ake kokarin sasanta kasashen don kawo karshen yakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng