ADC: 'Akalla 70% na Yan Najeriya Sun Dawo daga Rakiyar Shugaba Tinubu'

ADC: 'Akalla 70% na Yan Najeriya Sun Dawo daga Rakiyar Shugaba Tinubu'

  • Jam'iyyar adawa ta ADC ta sake caccakar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da ake tunkarar babban zaben 2027
  • ADC ta bayyana cewa abin kunya ne kashi 30 kacal na yan Najeriya ne suka gamsu da salon gwamnatin Shugaba Tinubu bayan shekaru uku a mulki
  • Ta kara da cewa galibin 'yan Najeriya ba su gamsu da gwamnatin Tinubu ba saboda matsin tattalin arziki, rashin ayyukan yi da matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar ADC ta yi magana kan alkaluman da suka nuna cewa kashi 30 cikin 100 na yan Najeriya ne ke tare da gwannatin Shugaba Tinubu a halin yanzu.

ADC ta ce hakan na nuna cewa yawancin ‘yan Najeriya sun yi watsi da gwamnatinsa saboda matsin tattalin arziki, rashin ayyukan yi da kuma matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @aonanuga1956, @BolajiADC
Source: Facebook

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Galibin 'yan Najeriya ba su tare da Tinubu

A cewar jam’iyyar ADC, sabon binciken jin ra'ayoyin jama'a daka gudanar, ya nuna kusan kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya ba su gamsu da yadda ƙasar ke tafiya ba.

ADC ta ce hauhawar farashin kayan abinci, raguwar ƙarfin sayen kayayyaki da kuma matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a sassan ƙasar ne suka jawo wannan rashin gamsuwa.

Jam’iyyar ta jaddada cewa bayan shekaru uku da Shugaba Tinubu ya yi yana mulki, ba zai iya ci gaba da dora alhakin matsalolin ƙasar kan gwamnatocin baya ba.

“Samun amincewar kashi 30 cikin 100 ba wata alamar nasara ba ce, illa wata shaida ce ta gazawa a fannin shugabanci,” in ji ADC.

Yadda mutane ke kallon mulkin Tinubu

Kara karanta wannan

Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

ADC ta ce binciken da kamfanin Eagle Badger Data Analytics (EBDA) ya gudanar ya nuna cewa kashi 30.2 cikin 100 ne kawai suka amince da yadda Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulki.

A gefe guda kuma, kashi 47.5 cikin 100 sun nuna rashin amincewa da aikinsa, yayin da mafi rinjayen ‘yan ƙasar suka bayyana cewa rayuwarsu ta kara tsananta tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Jam’iyyar ta ce wannan sakamako yana nuna cewa kusan mutum bakwai cikin goma a Najeriya ba su gamsu da alkiblar da ake tafiyar da ƙasar ba.

“Wannan ba ƙalubalen siyasa ba ne kawai, alama ce ta cewa jama’a sun yi watsi da wannan gwamnati,” in ji sanarwar.

A wani rahoton, kun ji cewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262