ADA: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Sabuwar Jam'iyyarsu Atiku da El Rufai

ADA: Abubuwa 5 da Ya Kamata Ku Sani game da Sabuwar Jam'iyyarsu Atiku da El Rufai

  • Gabanin zaɓen 2027, kungiyar NNCG ta gabatar da buƙata ga hukumar INEC ta rajistar sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna ADA
  • NNCG na ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
  • An ce INEC, wadda ke da kwana 30 domin kammala rajistar kowace sabuwar jam’iyya, ta karbi takardar buƙatar ƙafa jam'iyyar ADA

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Wasu ‘yan siyasa da ke kokarin kafa sabuwar jam’iyya mai suna All Democratic Alliance (ADA) sun aika da wasiƙa zuwa hukumar zaɓe ta kasa (INEC), inda suka nemi a yi wa jam’iyyar rajista.

Legit.ng ta tattaro cewa jagororin wannan sabuwar jam’iyyar na cike da kwarin gwiwa cewa hukumar za ta amince da bukatarsu tare da yi wa jam'iyyar rajista.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da ADA, sabuwar jam'iyyarsu Atiku, El-Rufai
Atiku, El-Rufai, da sauran 'yan adawa sun zaɓi sabuwar jam'iyya, sun sanya mata suna ADA gabanin 2027. Hoto: @Magixlamy_, @atiku
Asali: Twitter

Muhimman bayanai game da ADA

Jagororin kungiyar hadakar 'yan adawa da ke kokarin kafa sabuwar jam'iyyar domin kalubalantar APC da Shugaba Bola Tinubu a 2027 sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, a cewar rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi, da takwaransa na Kaduna Nasir El-Rufai, da jagoran kungiyar gamayyar ‘yan Arewa masu kishin dimokuraɗiyya, Umar Ardo, da wasu da dama.

Legit.ng ta haskaka muhimman abubuwa biyar masu ban sha’awa game da jam'iyyar ADA da ake so a yi wa rajista:

1. NNCG ke da ra’ayin kafa ADA

An yanke shawarar kafa ADA, kamar yadda za a rika amfani da sakandamayyarta ne ta hannun kungiyar hadaka ta Najeriya (NNCG).

Legit.ng ta fahimci cewa NNCG ce za ta dauki nauyin cikakken rajistar ADA.

2. Taken tafiyar ADA

Taken jam’iyyar da ake shirin kafawa shi ne: “Justice for All” (Adalci ga Kowa).

A Najeriya, jam’iyyun siyasa na amfani da taken yakin neman zabe don jawo hankalin masu kada kuri’a, saukaka fahimtar matsaloli, da kuma gina tunanin haɗin kai tsakanin ‘yan takara da magoya bayansu.

3. Tambarin ADA

ADA ta zabi masara a matsayin tambarinta, a hukumance. A baya an samu jam'iyyu irinsu da ANPP da suka yi amfani da alamar masara.

Tambarin jam’iyyar wanda aka zana da nufin nuna wadatar noma da karfafa matakin ƙasa, ya janyo an tuna da wasu kalaman da Shugaba Tinubu ya taba furtawa kan masara, abin da ya janyo martani daga ‘yan Najeriya.

Maimakon yabawa, tambarin ADA ya zama abin barkwanci a kafafen sada zumunta, inda hoton masara ya tuna wa mutane kalaman da Tinubu ya yi a shekarun 2021 da 2022.

4. Launin ADA

Launin jam’iyyar ADA ya haɗa da kore, ja da shuɗi.

Sai dai launin na kama da na jam’iyyar APC mai mulki, amma an bambanra yadda aka haɗa launukan da kuma hasken shuɗi da APC ke amfani da shi.

An ce Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai ne jagororin jam'iyyar ADA
Peter Obi, Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai na goyon bayan kafa sabuwar jam'iyyar ADA. Hoto: @peterobi, @atiku, @elrufai
Asali: UGC

5. Shugabannin riko da jiga-jigan ADA

ADA na da Akin Anderson Rickets, tsohon shugaban kwamitin hukumar tashoshin jiragen ruwa ta kasa (NPA), a matsayin shugaban riko na farko.

Abdullahi Musa Elayo daga jihar Nasarawa kuma shi ne sakataren riko na ƙasa.

Wasu fitattun ‘yan siyasa da aka ce suna tare da ADA sun haɗa da: Peter Obi, Aminu Tambuwal, John Oyegun, Rauf Aregbesola, Abubakar Malami, Babachir Lawal, Uche Secondus, Osita Chidoka, da Nnenna Ukeje.

Atiku ya yi martani kan kafa jam'iyyar ADA

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hadimin Atiku Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa 'yan haɗaka sun amince da ADA a matsayin sabuwar jam'iyyar hadaka.

Abdul Rasheeth ya bayyana cewa har yanzu 'yan haɗakar ba su zaɓi jam'iyyar ADA ba, saboda akwai batutuwan da ba su gama tattaunawa a kai ba.

Ya kuma buƙaci jama'a da su ƙara haƙuri, yana mai tabbatar musu cewa za a ba da cikakken bayani a lokacin da ya dace game da shirye-shiryen 'yan haɗakar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.