ADA: Atiku, El Rufai da Manyan Ƴan Adawa Sun Ƙirƙiro Sabuwar Jam'iyya gabanin 2027
- Daga karshe, haɗakar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ke jagoranta ta amince da ƙirƙiro sabuwar jam'iyyar siyasa
- Jagororin adawar Najeriya sun aika buƙatar yi wa jam'iyyar ADA rijista bisa tsarin doka ga hukumar zaɓe mai zaman kanta watau INEC
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi na cikin manyan ƴan siyasa da ke jagorantar haɗakar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jagororin adawa karƙashin haɗakar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ke jagoranta, za su kirkiro sabuwar jam'iyya.
Jiga-jigan adawar sun bayyana shirinsu na kafa jam'iyyar ADA, wacce za su yi haɗaka domin karɓe ragamar mulki daga hannun APC a zaɓe mai zuwa.

Asali: UGC
Jaridar Leadership ta tattaro cewa haɗakar ƴan adawar ta miƙa takardar bukatar yi wa jam'iyyar rijista a hukumnce ga hukukar zaɓe mai zaman kanta watau INEC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan adawa sun nemi rijistar sabuwar jam'iyya
Wasiƙar na ɗauke da adireshin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da sa hannun muƙaddashin shugaban ADC na ƙasa, Cif Akin Ricketts da sakatare, Abdullahi Musa Elayo.
Haka nan kuma wasiƙar na ɗauke da kwanan watan ranar 19 ga watan Yuni, 2025, sannan an raba wa manema labarai a yau Juma'a.
INEC ta karɓi wasiƙar a hukumance a ranar 20 ga Yuni, 2025, wacce aka yi wa taken, "Buƙatar rajistar jam’iyyar siyasa" tare da suna da tutar jam’iyyar ADA.
"Mun rubuto wannan takarda cikin girmamawa ga Hukumar INEC domin neman a rajistar jam'iyyarmu, wato All Democratic Alliance (ADA), a matsayin jam’iyyar siyasa," in ji wasiƙar.
Wadanda suka goyi bayan kafa jam'iyyar ADA
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na ɗaya daga cikin manyan da ke jagorantar hadakar ƴan adawa da nufin kayar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Daga cikin waɗanda suka goyi bayan ƙirƙiro jam'iyyar ADA akwai tsohon ministar sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi da Umar Ardo, jagoran kungiyar ƴan Arewa ta League of Northern Democrats.

Asali: Facebook
INEC ta yi magana kan rijistar jam'iyyu
Wannna na zuwa ne ne 'yan kwanaki kaɗan bayan INEC ta gargaɗi ƙungiyoyin siyasa cewa babu wata matsin lamba ko surutun jama'a da zai sa ta kauce wa bin ka'idar tsarin mulki da dokokin zaɓe.
Hukumar INEC ta sake jaddada cewa rajistar jam’iyyar siyasa wani tsari ne mai tsauri da ke karkashin doka, ba kawai sanarwa ko farfagandar siyasa ba ce.
Da wannan buƙata, haɗakar ƴan adawa ta kawo ƙarshen makonni na jita-jita game da ko za su farfaɗo da wata tsohuwar jam’iyya ko kuma su ƙirƙiri sabuwa daga tushe, rahoton Punch.
Wani matashi ɗan a mutun PDP, Kabir Dogo ya shaida wa Legit Hausa cewa wannan yunƙuri da su Atiku suka yi shi ne ya fi dacewa matuƙar ana son kayar da APC.
A cewarsa, duk inda Atiku Abubakar ya koma a siyasa, can za su koma domin suna da yaƙinin tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai kawo sauyi a Najeriya.
"Ina goyon bayan kafa sabuwar jam'iyya, kuma in sha Allah za mu kawo ƙarshen wannan mulkin mai kama da na kama karya, jama'a na shan wahala, amma ba abin da ake na gyara," in ji shi.
Atiku ya hango haɗarin da dimokuradiyya ke ciki
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana fargabarsa game da halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Najeriya.
Alhaji Atiku ya yi zargin cewa ƙasar na dab da fadawa cikin mulkin kama-karya, inda ake ƙoƙarin murƙushe duka jam’iyyun adawa.
Jagoran ƴan adawar Najeriya ya yi takaicin yadda wasu da suka samu dama ke kokarin ruguza dimokuraɗiyyar da aka sha wahala wajen rainonta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng