"Ba Su da Maraba," Hakeem Baba Ya Kwatanta Shugabannin Hadakar Su Atiku da APC
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Hakeem Baba-Ahmed ya soki shugabannin kawancen ‘yan adawa da ke neman kafa sabuwar jam'iyya
- Dr. Hakeem, ya yi zargin cewa jagororin na fifita bukatun kansu maimakon samar da ingantaccen sauyi da Najeriya ke bukata
- Ya bayyana cewa akwai rabuwar kai da rashin amincewa a cikin kawancen, inda ya ce tsofaffin ’yan siyasa ke riƙe da akalar tafiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon kakakin Kungiyar Northern Elders Forum, Hakeem Baba-Ahmed, ya soki tattaunawar da ake yi a tsakanin jam’iyyun adawa don kan kafa adawa da APC.
Yana wannan batu ne a lokacin da Shugabannin ’yan adawa suka mika bukata ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) domin samun rajistar jam’iyyar ADA kafin zaben 2027.

Asali: Facebook
The Cable ta wallafa cewa wannan yunkuri na neman kawancen adawa na samun jagoranci daga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Nasir el-Rufai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakeem Baba-Ahmed ya soki 'yan hadaka
A hira da Arise News, Baba-Ahmed ya bayyana damuwa kan yadda yan adawa ke wulakanta damarsu ta hanyar tara shugabanni da suka fi fifita buƙatar kansu a kan ci gaban kasa.
Tsohon mai bai wa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa ya ce akwai matsanancin rabuwar kai a cikin wannan kawance.
Dr. Hakeem Baba Ahmed ya kara da cewa matsalar tana da nasaba da shugabannin da ke jan ragamar lamarin ba tare da son sauka daga mulki ba.
Hakeem: 'Jama'a ba su aminta da hadakar adawa ba'
Hakeem Baba Ahmed ya kara da cewa yawancin ’yan Najeriya na cike da shakku kan wadannan shugabanni da ke kokarin kafa kawancen,
A cewarsa, har yanzu jama'a na jin haɗakar adawa ba za ta iya samar da wani sahihin sauyi ba idan aka kwatanta da gwamnatin Bola Tinubu.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Ba su da yakinin cewa ku kuke wakiltar wata sabuwar makoma da ta bambanta da wannan gwamnati; kawai kuna so ne ku sauya gwamnatin Bola Tinubu da ku."
“Babu wanda cikin waɗannan mutane ya kamata ya shugabanta ko a gan shi a matsayin wanda ke yanke hukunci kan wanda ya dace ya kasance cikin wannan kawance.”
Ya yi takaicin yadda hadakar ta cika da tsofaffin yan takarar shugaban kasa da gwamnoni, wanda a cewarsa babu yakinin za su samar da canjin da ake da bukata.
Hakeem Baba Ahmed ya shawarci yan adawa
A wani labarin, kun ji cewa Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya shawarci tsofaffin ’yan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi da su hakura da sake tsayawa a 2027.
Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da tsofaffin ’yan siyasar Najeriya za su ja gefe, su ba sababbin jini dama su fito su gyara kasa, ba su da aka saba jin duriyarsu ba.
Ya ce ba abin kirki ne ba a ci gaba da yawo da tsofaffin ’yan siyasa wadanda suka riga suka yi iya bakin kokarinsu, amma ba su kawo wani canji mai amfani ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng