Gwamnatin Kano Ta Bullo da Wani Shiri na Musamman da Zai Taimaki 'Yan Kannywood

Gwamnatin Kano Ta Bullo da Wani Shiri na Musamman da Zai Taimaki 'Yan Kannywood

  • Gwamnatin Kano ta bullo da wani shirin lafiya domin tallafa wa 'yan masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood
  • Shugabar hukumar KACHMA ta jihar Kano, Dr Rahila Aliyu-Muktar ce ta bayyana hakan a wani taro da aka shirya a hukumar tace fina-finai
  • Ta kuma sanar da cewa an yi wa wasu fitattun mambobin Kannywood guda takwas da ke fama da matsananciyar rashin lafiya rajista nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Hukumar Kula da Tsarin Inshorar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta kaddamar da wani sabon shiri domin inganta samun kulawar lafiya ga masu sana'ar fina-finan Hausa, wato Kannywood.

An bayyana shirin mai suna "Kannywood AbbaCare Initiative" a karkashin ajandar ci gaban harkokin lafiya ta gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Babban basarake a Kebbi ya samo mafita ga mutanensa kan matsalar 'yan bindiga

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a taron raba tallafi ga wasu kungiyoyin Kwankwasiyya Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugabar KSCHMA, Dr Rahila Aliyu-Muktar, ce ta kaddamar da shirin yayin wani taron fadakarwa da aka gudanar a hedkwatar Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano.

Dr. Rahila ta ce shirin ya zo ne domin yaba wa gudunmawar da 'yan Kannywood ke bayarwa wajen wayar da kan al'umma, bunkasa al'adu da kuma ci gaban zamantakewa.

Dalilin kirkiro shirin lafiya na Kannywood

Ta ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa marasa galihu a cikin masana'antar fina-finai ba su rasa damar samun ingantacciyar kulawar lafiya ba.

A cewarta:

"'Yan Kannywood na taka muhimmiyar rawa wajen gyara dabi'u a cikin al'umma. Ta hanyar wannan shiri, muna fadada tallafin kiwon lafiya gare su tare da tabbatar da cewa wadanda ke cikin bukata sun samu kulawar da ta dace."

Yan Kannywood 8 sun samu shiga

Shugabar KSCHMA ta kuma sanar da cewa an yi wa wasu fitattun mambobin Kannywood guda takwas da ke fama da matsananciyar rashin lafiya rajista nan take a karkashin shirin agajin gaggawa na RRT.

Kara karanta wannan

Hilda Dokubo: Jarumar fim ta yi wa Shugaba Tinubu tatas kan matsalar rashin tsaro

"Babu wanda ya kamata a hana shi magani saboda matsalar kudi. Wannan shiri an kirkiro shi ne domin tabbatar da cewa masu bukatar taimako sun samu kulawar lafiya cikin lokaci," in ji ta.
El Mustapha.
Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha Hoto: Abba El-Mustapha
Source: Facebook

Manufar gwamnatin jihar Kano

A cewarta, shirin ya yi daidai da hangen nesan Gwamna Abba Kabir Yusuf na samar da tsarin kula da lafiya wanda zai anfani dukkan bangarorin al'ummar jihar Kano ba tare da nuna bambanci ba.

Ta kara da cewa gwamnatin Kano na ci gaba da daukar matakan da za su tabbatar da cewa kowa ya samu damar samun ingantacciyar kulawar lafiya a Kano.

Abba ya amince da hade ma'aikatu 2

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hade wasu ma'aikatu wuri guda.

Gwamnatin ta sanar da haɗe ma'aikatar albarkatun ruwa da kuma ma'aikatar muhalli da canjin yanayi zuwa ma'aikata guda ɗaya tilo.

Gwamnatin Abba ta bayyana cewa matakin yana da nufin haɓaka ingancin gudanarwa, inganta haɗin gwiwar manufofi, da kuma gyara yadda ake amfani da albarkatu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262