Sule Lamido Ya Fadi Shirinsa don Kifar da Shugaba Tinubu a 2027

Sule Lamido Ya Fadi Shirinsa don Kifar da Shugaba Tinubu a 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya taɓo batun yunƙurin kifar da gwamnatin mai girma Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027
  • Sule Lamido ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga kowane irin shiri domin raba Shugaba Tinubu daga kan madafun ikon ƙasar nan
  • Tsohon ministan na harkokin wajen Najeriya ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da yin danniya tare da murƙushe ƴan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan batun kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

Sule Lamido ya bayyana cewa yana da niyyar shiga kowane irin yunkuri domin a kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Sule Lamido ya fadi shirin kifar da Tinubu
Sule Lamido ya ce zai shiga tafiyar kifar da Tinubu a 2027
Asali: Facebook

Sule Lamido ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise TV a ranar Asabar, 21 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan haɗaka sun zaɓi jam'iyyar taron dangi

A ranar Juma’a, haɗakar shugabannin jam’iyyun adawa suka amince da jam’iyyar ADA, domin ƙalubalantar jam’iyya mai mulki ta APC a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa nan gaba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne dai ke jagorantar haɗakar ƴan adawa don kawar da Tinubu da APC a zaɓen 2027.

Sule Lamido ya yi kalamai kan gwamnatin Tinubu

Sule Lamido, wanda mamba ne na jam’iyyar PDP, ya ce a shirye yake ya shiga kowace irin ƙungiya ko tsari, komai sunanta, matuƙar za ta taimaka wajen kawar da APC daga kan mulki.

Tsohon gwamnan ya kuma zargi gwamnatin Bola Tinubu da ƙoƙarin raba ƙasar nan tsakanin Arewa da Kudu..

Sule Lamido ya bayyana cewa ana amfani da ƙabilanci don ganin cewa an kawo rarrabuwar kawuna a tsakamin ƴan Najeriya.

Menene shirin Sule Lamido don kifar da Tinubu

“Ina cikin kowane irin haɗin gwiwa, komai sunanta, domin kifar da wannan gwamnati maras ƙwazo, maras tsaro, wadda ke raba Najeriya ƙarara tsakanin Arewa da Kudu daga kan mulki."
"Zan shiga kowane irin shiri don wannan manufa."
"Wannan gwamnati tana raba Najeriya bisa la’akari da ƙabilanci, tana amfani da hukumomin gwamnati wajen danniya, tsoratarwa da murƙushe ƴan adawa."
“Gwamnatin da ke kan mulki a yau ba ta wakiltar ƴan Najeriya ba ce, sai dai jam’iyyar siyasa kawai."
“Zan kasance cikin kowane irin shiri ko tsari idan hakan zai taimaka wajen cire wannan gwamnati daga mulki."

- Sule Lamido

Sule Lamido ya caccaki Bola Tinubu
Sule Lamido na son Tinubu ya rabu da mulki a 2027 Hoto: Sule Lamido
Asali: Twitter

Sule Lamido ya caccaki shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu kan jawabin da ya yi a bikin ranar dimokuraɗiyya.

Sule Lamido ya zargi shugaban ƙasan da ƙoƙarin sauya tarihi kan gwagwarmayar da aka yi dangane da ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa kalaman da shugaban ƙasan ya yi a ranar dimokuraɗiyyar wani yunƙuri ne na ɓata tarihin ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng