Tsohon Ɗan Takara a ADC Ya Fice daga Jam'iyyar, Ya Koma Layin Pantami a PDP
- Tsohon ɗan takarar majalisa a Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar ADC zuwa PDP mai adawa a Najeriya
- Ɗan siyasar ya bayyana cewa ya shiga PDP ne domin mara wa yunkurin Isa Ali Pantami kan jagoranci
- Ya ce Pantami ya nuna kwarewa wajen hidimar jama'a, tallafa wa matasa da inganta rayuwa, yana mai fatan hakan zai kawo ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pantami, Gombe - Tsohon ɗan takarar majalisar jihar Gombe ya sauya sheka daga ADC zuwa PDP mai adawa.
Ɗan siyasar, Hon. Mubarak Musa Dantori ya fice daga jam’iyyar tare da komawa PDP domin goyon bayan Isa Ali Pantami.

Source: Facebook
Dantori ya sanar da sauya shekar tasa ne cikin wata wasika da ya aika wa shugaban PDP na mazabar Pantami wanda ya wallafa a shafin Facebook.
Tasirin Dantori a mazabar Gombe ta Kudu
Mutane da dama na ganin komawar Dantori zuwa layin Pantami za ta karawa tafiyar karfi duba da tasirin da ya ke da shi musamman a yankin mazabar Gombe ta Kudu.
Dantori ya nemi takarar majalisar dokokin jihar Gombe karkashin ADC inda ya rasa takara yayin zaɓen fitar da gwani da ya ce an tafka rashin gaskiya.
Sanarwar ta fita ne jim kadan bayan ya tabbatar da murabus dinsa daga ADC, jam'iyyar da ya rasa takara.
Musabbabin komawarsa PDP a Gombe
Ya bayyana cewa matakin da ya dauka na shiga PDP ya samo asali ne daga kudurinsa na mara wa yunkurin “Pantamiyya” baya.
A cewarsa, wannan yunkuri wata kafa ce ta samar da nagartaccen shugabanci da kuma dorewar ci gaba a fadin jihar Gombe.
Dantori ya ce tarihin Farfesa Isa Ali Pantami a harkokin gwamnati, ayyukan jin kai da tallafa wa matasa ya sanya shi kama layinsa.
Ya kara da cewa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya nuna jajircewa wajen inganta rayuwar jama'a ta hanyoyi daban-daban.

Source: Twitter
Yadda Pantami ya taimakawa matasa a Gombe
A cewarsa, shirye-shiryen Pantami sun taimaka wajen samar da damammaki ga matasa tare da karfafa ci gaban tattalin arziki a jihar.
Dantori ya bayyana kwarin gwiwar cewa yunkurin Pantamiyya zai taimaka wajen samar da gwamnati mai rungumar kowa da kuma ci gaba.
Ya ce sabon matsayinsa na siyasa ya samo asali ne daga bukatar hada kai da shugabanci mai fifita hidimar jama'a.
Har ila yau, ya bayyana cewa ci gaban al'umma da bunkasa yankunan karkara na daga cikin manyan manufofin shugabancin da yake goyon baya.
'Yan ADC sun koma APC a Gombe
Kun ji labarin cewa 'yan jam'iyyar ADC a jihar Gombe na sauya sheka zuwa jam'iyyun APC, PDP da sauransu tun bayan zaben fitar da gwani da aka yi.
Sakataren jam'iyyar ADC a jihar Gombe, Dr Ahmad Gana ya sauya sheka zuwa APC, inda ya samu tarba ta hannun Jamilu Gwamna.
Wasu 'yan siyasa da suka nemi takara a karkashin jam'iyyar ADC, Dr Muhammad Bello da Mubarak Musa Dantori sun sauya sheka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

